MARABA DA ZUWA SHAFINMU NA MUSULUNCI

2 Oct 2007

I'ITIKAFI

I'ITIKAFI

Dasunan Allah mai Rahama Mai Jinkai

Shine lazimtan masallaci da zama cikinsa da niyyan samun kusanci zuwa ga Allah. kuma malamai sunyi ittifak'I -wato sun hadu- akan cewa itikafi an shar'antashi kuma mustahabbi ne.

Tunatarwa: wasu mutane na kuskure ta yanda suke daukan cewa Itikafi, yakebanci manzan Allah ne Sallalahu Alaihi Wasallam shi kadai, wasu kuma suce hadisin Itikafi an shafe shi, wasu kuma suna dauka cewa Itikafi na dattawane ko akasin hakan, to duk wadannan kurakurai ne ba'a sha. Nana A'isha Allah yakara yarda agareta tace: (Lallai manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yakasance yanayin Itikafi a cikin goma na K'arshe na Ramadan har Allah yadauki ransa, sannan matansa sukayi Itikafi a bayansa) Bukhari. Ibn Hjar yace (Ba'a shafe hadisin ba kuma baya cikin abubuwan da suka kebanci ManzanAllah Sallallahu Alaihi Wasallam)fathul baari 4/272.

HUKUNCIN ITIKAFI

Mafi yawan malamai sun tafi akan cewa mustahabbi ne.

Imamu Malik Yace: (Nayi tunani akan al'amarin Itikafi, da abinda yazo akansa, da yanda musulmai suka barshi, tareda cewa manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, be kasance yabarshi ba, se naga cewa sun barshi ne saboda yanada wahala akansu.)

Imam Azzuhri Yace: (akwai mamaki a Al'amarin musulmi! Sun bar Itikafi, tareda cewa Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, be barshi ba tunda yazo Madinah , har Allah madaukakin Sarki yadauka ransa.)

SHARUDDAN ITIKAFI

1. MUSULUNCI: baya inganta ga wanda ba musulmi ba.

2. HANKALI: mahaukaci baya itikafi, saboda koda ibada ta wajibi bata zama dole akansu ba, andaga alkalami akansu.

3. NIYYA: sharad'I ce ga dukkan ibadodi, kuma duk aikmin da babu niyya a cikinsa ba karbabbe bane.

4. MASALLACI: ga namiji dolene yayi a masallaci, amma mace kuma anyi sabani akanta, Malam SUHNUNU Yace: (nace ma ibnul K'asim: menene zancen Imamu Malik gameda Itikafin mace tayi amasallacin jama'a? se yace Na'am, yace: a zancen Malik tayi Itikafi a masallacin gidanta? Se yace: Hakan baya burgeni, ana itikafi ne a masallacin da'aka yishi dan Allah.) Mudawwana 1/295.

Sheikh Aminul Hajj yace: (amma yafi rinjayen dalili awurina shine mace tayi Itikafinta a gidanta, wato wurin da takebance shi tana sallah a cikinsa.

5. AZUMI: wasu daga cikin malamai sukace kada mutum yayi itikafi face yaname Azumi, an tambayi Ibnul K'asim: (shin anayin itikafi batare da azumi ba a cikin zancen Malik? Se yace: ba'ayi se da Azumi. Wasu kuma sukace anayi koda mutum beyi Azumi ba, Sukace wannan shine ra'ayi mafi rinjayen dalili, saboda Hadisi Umar ingantacce da Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya Umarce shi da yayi itikafi yayin da yace masa yayi alwashin yin hakan a jahiliyya, kuma be ce masa yayi Azumi ba.

6. IZINI: dolene se miji yayi wa matarsa izini ko abinda ya mallaka na bawa ko baiwa, miji mace yana gida ne ko yayi tafiya dole tanemi izininsa, kuma idan yayi mata izini, to be kamata ya hanata ba kuma.

RUKUNNAN ITIKAFI

1. Zama a cikin Masallaci. 2. Nisantan Jima'I da abubuwan da zasu iya kaishi yin hakan. 3. Nisantar manyan laifuka. 4. Musulunci. 5. Hankali. 6. Tsarki daga Haila. Itikafi yana baci saboda rashin daya daga cikin wadannan.

ABUBUWAN DASUKE BATA ITIKAFI

1. FITA DAGA MASALLACI: baya halasta fita daga masallaci, In banda fita saboda: dan Biyan bukata kamar fitsari ko bayan gari, wankan janaba da na jumu'ah, cin abinci ko abin sha idan be iya ci ko sha a wurin da yake itikafi, idan yaji tsoron wuta ko sata kom rushewan gini, in aka fitar da shi da karfi, idan mace tayi haila da sharadin ta dawo da tayi tsarki, idan mijin mace yarasu ko yasake ta zata fita a mafi rinjayen zancen malamai biyu wasu sukace zata cigaba har seta kammala, fita saboda yin Umara, fita da mantuwa, idan yayi hauka ko suma.

2. YIN JIMA'I: saboda Allah yace: (kuma kada ku sadu dasu, alhalin kuna masu Itikafi a cikin masallatai…) Sur.Baqarah-186. haka sun bantan mace da sha'awa.

3. YIN RIDDA:wato fita daga musulunci

4. YIN MANYAN LAIFUKA: kamar yin zina da sata acikin itikafi, wanda mutane suna sakaci da daukan abin wani ko da kadan kuwa se a kiyaye.

5. YIN HAUKA KO SUMA: yana bata itikafi se dai idan yasami lafiya ko ya farfad'o to se yacigaba.

6. HAILA: idan mace tayi haila itikafinta ya baci, amma idan tayi tsarki se ta cigaba, na bayan be baciba.

ABUBUWAN DA BA'ASO GAME ITIKAFI

Ba'aso me itikafi ya shagaltu da abinda ba ambaton Allah ba, da kuma abinda ba dolene ba.

1. jayayya. 2. zagi damaganganun banza. 3. Yin giiba da Annamimanci. 4. Kallon abinda yake haramun. 5. Rashin yin magana gaba daya tun daga safe har dare da sunan bauta.

Tunatarwa: wasu daga cikin daliban ilimi se kaga suna zuwa itikafi da wasu littafai na karatunsu suna yin muraja'a, ba haramun bane amma kamata yayi tunda kwanakine yan kadan a cikin shekara, meze sa bazakayi hakuriba, sauran kwanakin shekara kayi acikinsu.

ABUBUWAN DASUKA HALASTA GAME ITIKAFI

1. Yin wanka da canza kaya, da sanya kayan da yakeso.

2. Cin Abinci da Shan Abin Sha a cikin masallaci.

3. Yin magan da yan uwa, amma ba'ason yawaita surutu da mutane.

4.Ya nemi Aure ko a daura masa Aure.

5. Yin Aski da yanke Farce.

6. Sanya turare.

ABUBUWAN DA SUKE MUSTAHABBI GA ME ITIKAFI

1. Mustahabbi ne ga me itikafi, yakafa tanti da ze kangeshi daga jama'a, inbe samu ba se ya lazimce wurin da babu jama'a ta yanda baze barshi ba seda larura.

2. kiyaye yin Sallah cikin jama'a, da nafiloli.

3. Yawan karatun alk'ur'ani, da rashin shagaltuwa da abinda ba ruwa.

4. Yawan ambaton Allah, zikiri, da tasbihi.

5. Yin azumi a cikin wantan da ba ramadan, ga wanda zeyi itikafi da rana.

6. Yawan yin kokari wajen d'a'a.

MAFI KARANCIN ITIKAFI DA MAFI YAWANSA

Itikafin neman lada baya da kad'an ko mafi yawa, se dai wanda yayi Itikafi a goman k'arshe na Azumin kada ya fita se idan anga watan Sallah wato Shawwal, malamai sun hadu akan cewa baya da mafi yawa, amma sunyi maganganu akan karancinsa, wasu sukace mafi karancinsa Sa'a, wasu sukace Yini daya da dare, wasu sukace kwana goma.

Imamul k'urtabi yace: ( mafi karancin itikafi a wajen Malik, da Abu Hanifa, dare da yini….)

YAUSHE AKE SHIGA ITIKAFI KUMA YAUSHE AKE FITA

A. Shiga wajen itikafi:akwai zancen malamai guda biyu:

1. Shiga bayan sallar Asubahin ranar Ashirin da d'aya na Ramadan, saboda hadisin Nana A'isha Allah yakara mata yarda tace: (Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam idan ze shiga itikafi yana yin sallar Asubahi, sannan se yashiga wurin itikafinsa) Bukhari. kuma wannan shine mafi rinjayen dalili. Kuma mazhabinAhmad da Laith da Ishak'.

2. Shiga kafin rana r daren Ashirin da d'aya ta fad'i, wannan shine mazhabin Malamai hud'u

B. Fita daga itikafi: Ana fita daga wurin itikafi bayan ganin watan sallah, wasu kuma sukace mustahabbine ya bari har yayi sallar idi sannan ya tafi.

SIRRIN DA YAKE CIKIN I'ITIKAFI

Bauta tana da sirruka da hikimomi masu yawa, saboda ayyuka gaba daya, makewayansu itace Zuciya, kamar yanda Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Yace (..Kusaurara! lallai acikin jiki akwai wata tsoka wanda idan ta gyaru, to dukkan sauran jiki ya gyaru, kuma idan ta bace, to dukkan Sauran jiki ya baci, ku saurara! Itace zuciya.) Bukhari da Muslim.

To in muka duba zamuga cewa mafi yawan abubuwan da suke bata zuciya, sune sha'awan cin abinci da abin sha da saduwa da Iyali da Zancen da ba na dole ba, da barcin da ba na dole ba, da abokai da basu da wata fa'ida da sauran abubuwa dasuke kawar da zuciya daga yin abinda yake biyayya ne ga Allah, se Allah ya Shar'anta wasu abubuwa na lada da zasukare zuciya daga rud'ani da shagaltuwa daga ambaton Allah, kamar Azumi wanda yake hana mutum cin abinci da abin Sha da Saduwa da Iyali da rana. To wannan hanuwan daga wadannan abubuwan jin dadi, shine yake karfafa alak'a tsakanin mutum da Ubangijinsa, da fuskantar dashi ga Lahira, kena Azumi garkuwa ce datake kare zuciya daga abubuwan sha'awa da suke kawar da mutum daga yin biyayya ga Allah, duk da hanine wanda yake matsakaici saboda an halasta wa mutum wadannan abubuwa a cikin dare.

To haka shima Itikafi yanada Sirri me girma, shine Kare mutum daga yawan cakud'a da jama'a, da yawan magana, saboda me Itikafi yana shagaltuwane da karatun Alk'ur'ani da Tsayuwa –wato yin sallah- da Zikiri da yawan yin Addu'a da makamantansu, haka kuma akwai kariya daga yawan barci, tunda yazo ibada ne ba barci ba, to wadannan abubuwa barinsu shike kara sa zuciya ta fuskanci Allah.

ABUBUWAN TUNATARWA

* Wasu daga cikin malamai sun tafi akan cewa ba'ayin Itikafi se a masallatai guda Uku kamar yadda yazo a cikin Hadisi, na hani akan yin Itikafi a masallatan da basuba, manzan Allah Sallalahu Alaihi Waasallam yace (Babu Itikafi face a masallatai guda uku) imamu Tahawi. -Wato masallacin Harami wato Ka'abah da masallacin Madinah da masallacin Aqsa wato Kudus-, Malamai suka fassara shi da cewa hani ne na yin alwashin yin Itikafi a wani masallaci da tafiya zuwa gareshi saboda hakan se a wadannan masallatan kadai ya halatta, ayi hakan saboda duk malaman mazhabobi Hud'u sun hadu akan cewa ya halatta ayi a kowani masallacin Juma'a.

* wasu sukan bar ayyukansu na wajibi saboda suyi Itikafi, to yin hakan kuskure ne saboda shi Itikafi sunna ce, saboda haka ba'a barin abinda yake wajibi saboda Sunnah.

Ya Allah Ka Karba mana dukkan Ayyukanmu a cikin Watan Ramadana kasa Muna cikin Bayinka Yantattu dag Wuta kuma kadatarmu da daren Lailatul K'adari. Amiin

20 Sept 2007

Yin Busahara da Azumin Ramadana

Yin Bushara da Azumin Ramadan
Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya kasance yana yima Sahabbansa Bushara da shifa watan Ramadankamar yadda Imamu Ahmad da Imamu Nasa'I suka kawo Hadisin da Abu Hurairah ya ruwaito daga Manzan Allah Sallalahu Alaihi Wasallam yace manzan Allah yakasance yanayiwa Sahabbansa Bushara "Hak'ik'a watan Ramadana mai albarka yazo maku, Allah ya wajabta maku Azumtansa, Ana bud'e kofofin Aljanna acikinsa kuma ana kulle kofofin Wuta , kuma ana D'aure Shaidanu acikinsa, akwai dare da tafi wata dubu acikinsa…………"
Watan Ramadan Yanada Wadansu Falala:
1. Watan da'aka Saukarda Alk'ur'ani 2. watan Taraawih da Tahajjud. 3. Watan Tuba da Kankare Zunubai. 4. watan Daure Shaid'anu. 5. watan da'ake kulle kofofin Wuta. 6. watan da'ake bud'e kofofin Aljanna. 7. watan kyauta da Ihsani. 8. watan da'ake y'antawa daga wuta. 9. watan Lailatul K'adr. 10. watajnAddu'a. 11. watan Jihadi. 12. watan da'ake nunka Lada acikinsa. 13. watan Hak'uri da Godiya.
Wata Me Tarihi
Watan Ramadan Watane me Tarihi acikin Musulunci wanda acikinsa aka Samu da yawa daga cikin Nasarorin yak'i da Kafirai. Gasu kamar haka: Shekar Ta Farko: acikin Ramadan aka aika Sariyya ta farko k'ark'ashin jagorancin Hamza bn Abdulmutallib, se Sariyyan Ubaidah binil Harith, domin sanya tsoro acikin zukatan Kafirai. Shekar Ta Biyu: acikin Sha bakwai ga Ramadan akayi Yak'in Badar Alkubra. Shekar Ta Uku: a cikin Ramadan manzan Allah Sallahu Alaihi Wasallam ya Shirya Runduna a madinah domin su hana mushrikai dasuke son daukan Fansan Yak'in Badr. Shekar Ta Biyar: Shiryawa Yak'in Khandaq, anyi yak'in ne acikin watan Shawwal wato watan Sallah kamar yanda Imamu bnil Qayyim yace Sun shirya mashi da wata d'aya wato suna hakk'a ganuwa. Shekar Ta Shida: Sariyyan Gaalib bin Abdullah wanda ta kunshi mutum da'ri da talatin wanda sukayi nasara akan bani Abdullahi bn tha'alabah. Shekar Ta Takwas: Bud'e Makkah acikin Ashirin ga Ramadan Allah ya daukaka Addininsa da manzansa da muminaikuma ya tseratar da Dakinsa me alfarma daga Hannun Mushrikan K'uraishawa, manzan Allah Sallalalhu Alaihi Wasallalm ya Shigeta tare dashi akwai Sojojin Musulunci dubu Goma. Shekar Ta Tara: Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam shi da Sahabbaqnsa suka dawo daga Ykin Tabuka. Shekar Ta Sha Uku: Yak'in Buwaib yakasance cikin ramadan a wuri da ake kira Buwaib kusa da kufa a yau acikin k'asar Iraq inda Farisawa karkashin jagorancin Mahran da musulmai Karkashin Jagorancin Almuthanna bin Harithah wanda yaki me matikar muni ya afku daga karshe Allah yaba musulmai nasara, an kashe da dama daga cikin musulmi, sukuma Farisawa tsakanin wanda aka kashe da wanda suka fad'a cikin ruwan Furat wajen gudu kimanin Dubu D'ari kuma aka samu Ganima me yawa, daganan ne aka karya Lagwan Farisawa. Sannan se Bud'e Garin Nuuba, a kudancin masarkarkashin Jagorancin Abdullahi bin Sa'ad bin Abi Sarah, wandA hakan ya bud'e kofa ga muslunci wajen Yad'uwa a garuruwa da yawa. Shekar Ta 53: Bud'e TsibirinRuuds, a karkashin Junadah bn Abi Umaiyah. Shekar Ta 67: Aka Gusar da daular Mukhtar Athak'afi wanda aka kashe a sha hud'u ga ramadan karkashin jagorancin Gwamnan Basra Mus'ab bini Zubair. Shekar Ta 91: Bud'e Andalus a hannun D'arik' bin Yazid bawan Musa dan Nusair sannan se Yak'in D'urif, musa bin Nusair ya aika wani mutum daga cikin K'abilar Bar-Bar ana kiransa D'uraif da mutane dari hudu da dawakai dari, inda suka tafi suka kai farmaki a gefen tekun Andalus kuma suka dawo da nasara. Shekar Ta 102: Musulmai suka bud'e Faransa bayan sun kafu a Andalus wato Spain kenan, se suka fara yakan Arewaci da yak'I abayan duwatsun pranis wanda suke tsakaninn Andalus da Faransa wanda da yawa daga cikin dakaru suka jagoranta. Acikin dan wannan gajeren lokaci baze yiwu mu iya ambatan duk yakin da'akayi cikin Ramadana ba ko bayanai sosai gameda hakan, kawai munso bayyana wasu daga cikine kawai dan nuna muhimmancin wannan wata da tarihinsa wajen musulmi.

26 Aug 2007

Falalar Ramadan

Falalar Azumin watan Ramaadan Hadisi tabbatacce yazo cikin bukhari da muslim daga Abu Hurairah Allah yakara masa yarda yace"Manzan Allah Sallalahu Alaihi Wasallam Yace (Dukkan aikin dfa dan Adam yayi to nasane Duk aikin lada yanada guda goma makamancinsa, har zuwa a ninka masa sau dari bakwai,se Allah madaukakin Sarki yace: banda Azumi domin shi nawane kuma nine zansaka akansa, shi me Azumi yakame daga Sha'awarsa da abinci da abin sha saboda ni, me Azumi yanada Farin ciki guda biyu: farin ciki a lokacin daze sha ruwa da farin ciki lokacin gamuwa da ubangijinsa, kuma tabbas warin bakin me Azumi shi yafi dadi a wurin Allah akan Kanshin turaren Almiski). Allah ya kebance Azumi a wannan riwaya daga cikin ayyukan daake rubanyawa daga goma har zuwa dari bakwai saboda Azumi baya da adadi wajen Rubanyawa Allah shi yasan Adadin daze rubanyashi, domin shi Azumi yana daga cikin hakuri, Allah madukakin Sarki yace: ("Lallai Allah yana cikawa masu Hakuri ladansu ne batare da Iyakancewa ba"Sur. Zumar-10) kuma yazo cikin hadisi manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ma'anar Fadansa (Azumi nawane) ya jingina Azumi zuwa gareshi ne saboda acikin azumi akwai hana rai abinda aka haliccieta da

11 Aug 2007

TAUHIDI (kadaita Allah)

Dasunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai
TAUHIDI (kad'aita Allah)
Shine kadaita Allah a cikin Bauta shi kadai batare da hadashi da wani ba, kuma shine Addinin da aka aiko Annabawa dashi gaba dayaAllah yakara masu Aminci, kuma Allah baze karbi wani Addini ba inba shiba, kuma baya karban Ayyukan bayi se dashi, domin shine Asalin da ake gina Addini akanshi, kuma duk sanda aka rasashi to aikin bawa baze amfane shiba. KARKASUWAN TAUHIDI Tauhidi yakasu zuwa kashi uku (3):
1. Tauhidin Rububiyyah (Reno) Shine kudurce cewa Allah, shine wanda ya halicci, dukkan halittu, yake azurtasu, kuma wannan Nau’i na Tauhidi babu wanda yake musunshi, har mushrikan farko sun tabbatar dashi, kamar su Abu Jahal, fir’auma ne kawai wanda yatabayin musun babu ubangiji, sun kasance suna shedawa cewa Allah shine wanda yake halitta, yake gudanar dakomai dake cikin duniya, shike rayawa, yake kashewa, Allah madaukakin Sarki yace “Kuma idan kuka tambayesu wanene wanda yahalicci Sammai da Kassai, yake gudanar da Rana da Wata? Tabbas zasuce maka shine Allah…..( Sur.Ankabut: 61) Se ikirarin dasu kayi be shigar dasu musulunci ba, kuma baze tseratar dasu daga Azaba ba, kuma bata kare masu dukiyoyinsu da dukiyoyinsu ba, saboda basu tabbatar da Tauhidin Uluhiyyah, sun hada Allah da wani cikin bauta.
2. Tauhidin Uluuhiyyah (Bauta) Shine kadaita Allah acikin dukkan Ayyukan bauta da ake kusanci zuwa ga Allah dasu, kamar Addu’a da Tsoro,da Fata, da Dogaro, da Kwadayi, da Tsorata, da Neman temako, da neman biyan bukaya, da yin yanka da Alwashi da makamantansu. Kuma Allah yasaukarwa manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam (“Kace an umarceni ne da in bautawa Allah ina me kadaita masa Addini” Sur. Zumar 11.) wato bauta Saboda haka mutum baze juya wani daga cikin ibada bag a wani daya daga cikin mala’iku ko wani Annabi ko wani Waliyyi ko Shehi, domin hakki ne na Allah, wanda kon yaba wanda bashi ba to yayi Shirka.
3. Tauhidin Asmaa’u was Siffat Shine imani da cewa Allah yana da zati wanda baya kama da sauran zatuttuka, yana da siffofin da b asa kamada sauran siffofi, kuma sunayensa suna nuni ne nuni na yanke shakka akan abinda abinda yake dashi na siffofin cika wayo kamala kai tsaye. Allah Subhanahu Wata’ala yace (“Babu wani abu da yayi kama dashi kuma shi me jine me gani “ Sur. Shuurah 11.) kuma da tabbatar da abinda Allah ya tabbatar ma kansa acikin littafinsa (Al’qur’ani)ko manzansa yatabbatar masa dashi tabbatarwa wacce take dacewa da girma da daukakarsa ba tare da kamantashi da wani abu ba, ko kwatantashi da wani ba, ko kore masa sifar, ko lankwasa ma’anarsa, ko yanda yake, baza muyi kokarin kamanta wani sashi na cikin siffofinsa ba da zukatanmu ko da tunaninmu, A’ah zmu bar abin kamar yanda yabamu labari. TO YAYA ZAMU SAMU TAUHIDI?
Zamu iya zama masu tauhidi ne, ta hanyar sanin Allah, wanene shi? da sanin hakikaninsa, a ilmance da kuma aiki da hakan, kuma shine Rai tajawu ko zuciya zuwa gareshi da soyaiya, da tsoro, da komawa zuwa gareshi, da dogaro akanshi, da Addu’a, da tsarkakeshi, da girmamashi da kuma yimasa bauta. Atakaice dai kada yazamana a zuciyar dan Adam daba na Allah ba, kuma bawa yazama baya nufin Allah da Shirka ko Bid’ah ko Sabo karaminsa da babbansa,kuma kada ya nuina kiyaiya ga duk abinda Allah yayi Umarni dashi to wannan tauhidi da kansa wato Laa ilaa ha illal Lah. MENENE MA’ANAR LAA’ILAA’HA ILLAL LAHU?
Ma’ana shine babu abin da’ake bautawa da cancanta a Sama da Kasa face Allah shi kadai baya da abokin taraiya, domin abubuwan da’ake bauta mawa baatattu suna da yawa, se dai abinda ya can-can ci bautan shine Allah shi kadai.Allah Subhanahu Wata’ala yace: (“ Saboda haka Allah shine Ubangiji na gaskiya, kuma tabbas an\binda suke kira wanda bashi baataccene, kuma lallai Allah shine madaukaki kuma me girma” Sur.alhajj:62) ba ma’anarta ba Babu mahalicci se Allah kamar yadda wadansu jahilai suke tsammani, domin kafiran Kuraishawa wanda Allah ya’aikoda manzo a cikinsu sun kasance suna sheda cewa Allah shine mahalicci me gudanar da al’amuran duniya shi kadai baya da abokin taraiya kamar yanda Allah yace: (“Shin yanzu za’a sanya Abin bauta yazama ubangiji guda daya Lallai wannan abune me ban mamaki” Sur. Saad:5) sun fahimci cewa wannan kalma lallai tana bata bautawa duk wanda ba Allah ba, kuma tana takaita bauta ga Allah shi kadai sukuma basa son haka, saboda hakane manzan Allah ya yakesu har se sun Shaida da Laa ilaa ha illal laahu kum subata hakkinta, shine kadaita Allah da bauta shi kadai. Wanna ke bata ikirarin da wadansu keyi cewa ma’anar Laa ila ha illal laahu shine kace Allah yana nan kuma shine wanda yayi halitta, yake gudanar da al’amura kuma wanda yayi hakan yana da Tauhidi koda yayi ma wani bauta kamar Rokon wadanda suka mutu suke cikin kabari,d yimusu alwashi, da neman kusancinAllah tahanyarsu, da neman Albarka (tabarruki) da yin dawafi a kabarbura da neman albarka da kasar kabarin kamar yanda muke ganin a kabarin Shehu dan fodio dake sokoto. Hakika kafiran Kuraishawa sun san cewa Laa ilaa ha illal lahu tana bukatan aiki shine barin bautawa wanda ba Allah ba, kuma idan suka fadeta suka cigaba da bauta ma gumaka to zasu war-ware musuluncinsu sukuma bas son haka sukeba, abin mamaki yau zaka musulmi suna bauta ma Allah kuma suna neman temakon wanda ba Allah, suna kiran sunayen wasu matattu na mutanen kwarai, suna war-ware musuluncinsu. Tur da wanda Abu jahal, da Abu lahab suka fisu sanin ma’anar laa ilaa ha illal lahu. RUKUNNAN KALMAR TAUHIDI
Kalmar tauhidi tana da rukunnai guda biyu (2). korewa: tana kore bautan kowani irin abin bauta. Tabbatarwa: tana tabbatar da bauta ga Allah madaukakin Sarki shi kadai batareda hadashi da wani ba. MENENE KE WAR-WARE KALMAR TAUHIDI?
Abubuwan dasuke war-ware (bata) Kalmar tauhidi suna da yawa, amma ga wadansu daga ciki:
Na Farko: Shirka da Allah a cikin bauta, Allah madaukakin Sarki yace: (“Lallai Allah baya gafartama wanda yahada shi dawani, amma yana gafarta ma abinda ba haka ba (shirka) ga wanda yaso” Sur.Nisaa’i:116) kuma yace: (“lalai ne duk wanda yayi Shirka da Allah, to hakika Allah ya haramta masa Aljanna, kuma makomansa itace wuta, kuma Azzalumai basu da wani me temako” Sur.ma’idah:72) kuma yana daga cikin shirka, kiran wani da ba Allah ba, Idan wata musiba (fitina) tazo, yi ma Aljanu yanka ko kabari.
Na Biyu: Duk wanda yasanya wani tsakaninsa da Allah, yana Rokonsu, yana kiransu, yana neman cetonsu, yana dogaro a kansu, ya kafirta da ijmaa’in malaman musulunci.
Na Uku: Duk wanda be kafirta mushrikai ba ko yayi shakkan kafircinsu, ko yake gyara abinda suke akai kaman yan gurguzu. To ya kafirta.
Na Hudu: Duk wanda yake kudurin cewa shiryawan da ba ta Annabi ba, shi yafi cika da dai-dai akan shiryarwar manzan Allah Sallal lahu alaihi wasallam, ko hukuncin wani yafi hukuncinsa, kamar wanda yake fifita tsarin turawa akan Shri’ar musulunci to ya kafirta.
Na Biyar: Duk wanda ya kyamaci wani daga cikin abinda manzan Allah yazo dashi to koda yayi aiki dashi ya kafirta Allah madaukakin Sarki yace (“Hakan saboda kafirai sun kyamaci abinda Allah ya saukar se yabata ayyukansu”Sur.muhammad:9) Na Shida: Duk wanda yayi izgili da wani abu dake cikin Addinin da manzon Allah yazo dashi, ladan dake ciki, ko azaban dake ciki ya kafirta Allah madaukakin Sarki yace (“kace masu shin yanzu da Allah, da Ayoyinsa, da manzansa kuke yiwa izgili? Kada kukawo uzuri hakika kunzama kafirai bayan kuna masu imani...Sur.tauba:65-66)
Na bakwai: Sihiri duk wanda ya aikatashi ko ya yardaq dashi,ya kafirta Allah madaukakin Sarki yace: (“ kuma basa karantar da kowa sihiri – aljanu – face .........................................................................................
Na takwas: duk wanda.............. zamu cigaba isha Allah

6 Aug 2007

Shi yasa aka fifitasu....

Dasunan Allah mai Rahama mai Jinkai WADANSU ABUBUWA DA'AKA KEBANCE AL'UMMAR MUSULMI DASU AKAN SAURAN AL'UMMU Hakika Allah madaukakin Sarki ya karrama A'ummar musulunci, kuma ya daukakata akan sauran al'ummu, ya kebanceta da wasu abubuwa, ita kadai. Tabbas tasami wannan girmane, saboda daraja da falalan Annabinta Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam, da imani datayi dashi. Daga cikin daukakashi da Allah yayi bayan yazabeshi daga cikin halittu,ya zaba masa Abokai (wato sahabbai) matemaka agareshi. Allah madaukakain Sarki yace ( "shine wanda yazabeku –sahabbai- kuma be sanya maku wani abu me wahala acikin Addini ba" ) (Sur. Hajji -78.) kuma yace ( "kuma haka muka sanyaku Al'umma mafificiya domin kuzamo masu sheda ga mutane (Annabawan dasuka gabata akan mutanensu) kuma manzo yazama me shesa akanku….") Sur. Baqarah-143). Saboda haka ne yazama dole akan muslmai dasusan abinda suke ciki na ni'ima,da kuma abinda suke akai na alkhairi, don suyi rikoda shi kumasuyi rikodashi kuma suyi aiki domin yadashi……………………….zamu cigaba insha Allah

4 Aug 2007

MATSAYIN SALLAH

Dasunan Allah Mai Rahama Mai Jinkaiِ
SALLAH
Ita Dayace daga cikin rukunnan musulunci guda biyar, wanda Allah maduakakin sarki ya wajabtata guda Hamsin(50) yayin da manzan Allah Sallallaahu Alaihi Wasallama yaje Mi'iraaji (wato Sama) yakarbo ta yayi ta neman ubangiji da ya ragemana ita har aka rageta zuwa guda biyar (5) kamar yadda take a yau saboda tausayin manzan Allah garemu Sallalahu Alaihi Wasallam. Kuma manzan Allahn Sallalahun Alaihi Wasallam yace "Itace farkon abinda za'ayi Wa bawa sakamako (hisabi) Ranar k'iyama Idan tayi kyau dukkan Sauran aiki zasuyi kyau bawa yasama tsira kuma idan tayi muni to dukkan sauran ayyuka bazasu amfane bawaba. Sannan kafin Sallar da bawa yakeyi tasami karbuwa se idan tadace da yadda manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yayita kuma ya karantar domin fadan Ma'aiki "Kuyi Sallah Kamar yadda kuka ina yin Sallah", Sannan an wajabta yinta acikin jama'a (wato Jam'i a masallaci). Kuma wanda duk yabarta to yabar musulunci kamar yadda ma'aiki Tsira da Amincin Allah su kara Tabbata Agareshi yace " Alkawarin dake tsakaninmu dasu shine Sallah duk wanda yabarta to ya kafirta". To idankowannan shine al'amarin Sallah to yazama dole akan kowane muslmi dayasan mecece Sallah? Kuma menene Hukunce-Hukuncenta? da abubuwan dasu batata domin ta kasancce karbabaiya a wajen Allah Madaukakin Sarki…………….

MABUDI

Dukkan yabo da Godiya sun tabbata ga Allaah madaukakin sarki Tsira da Amincin Allaah su kara tabbata ga manzan Allaah da Iyalan gidansa da duk wadanda suka bi karantarwarsa wato sunnarsa har zuwa ranar sakamako. Amin