MARABA DA ZUWA SHAFINMU NA MUSULUNCI

9 Feb 2008

HANYOYIN TABBATUWA AKAN ADDININ ALLAH NA (2)

NA BIYU: BIN DOKOKIN ALLAH DA AYYUKA NA KWARAI:

Allah Madaukakin Sarki Yace: [Allah yana tabbatar da wadanda sukayi Imani da zance tabbatacce a rayuwar duniya da kuma a lahiha kuma Allah yana batar da Azzalumai kuma Allah yana aikata abinda yaga dama] [Sur.Ibrahim -27]. Imamu Qadata Yace: “Abin nufi da a rayuwar duniya shine: ya tabbatar dasu akan alkhairi da aiki na kwarai, kuma abin nufi da: a lahira wato a cikin kabari”, kuma an ruwaito hakan daga fiye da mutum daya, daga cikin magabta [Tafsirin Ibn Kathir Vol.4 p.421.] Kuma Madukakin sarki Yace: [Da’ace sun aikata abinda akeyi masu wa’azi, da hakan yazama alkhairi agaresu, kuma da yafi k'arfi wajen tabbatarwa] [Sur. Nisa’i-66]. wato akan gaskiya. Kuma wannan a bayyane yake, in ba haka ba, Shin muna tsammanin samun tabbatuwa daga wajen masu kasala, wadanda basa aikata ayyuka na kwarai a lokacin da fitina zata turo kanta, kuma huduba zata……..? Amma wadanda sukayi Imani kuma sukayi aiki na kwarai Ubangiljinsu ze shiryar dasu zuwaga tafarki na kwarai saboda Imaninsu, domin haka ne Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya kasance yana yin Umarni da dauwama akan ayyuka na kwarai, kuma aikin da yafiso shine wanda aka dauwama akansa koda ko dan kadas n ne, kuma haqka Sahabbansa sun kasance idan sukayi wasni aiki to suna tabbata akansa.

Nana A’isha Allah yakara Yarda agareta, ta kasance, idan ta aikata, wani aiki tana lazimtarsa. Kuma Ma’aiki Sallallahu Alaihi Wasallam Ya kasance Yana cewa: “Duk Wanda ya dauwama akan yin Raka’a goma sha biyu to Aljanna ta tabbata agareshi” [Tirmidhi Vol.2 No. 273 Nasa’I Vol.1 No. 388]. (Abin Nufi: Nafiloli da'akeyi kafin salloli na farilla da bayansu), kuma yazo cikin Hadisi Qudusi: “kuma bawa baze gusheba yana kusantuwa zuwa gareni, da aikata Nafiloli har in so shi” Bukhari.

NA UKU: TADABBURIN (YIN TUNANI AKAN) K’ISSOSHIN ANNABAWA DA BINCIKE AKAN HAKAN DOMIN YIN KOYI DA AIKI: Kuma dalili akan haka Fadansa Madaukakin Sarki: [ Kuma kowanne daga cikinsu muna baka K’issarsa, daga labarin Manzanni gwargwadon abinda zamu tabbatar da zuciyarka dashi, kuma akan hakan Gaskiya tazo maka da wa’azi da tunatarwa ga Muminai] [Sur. Hud – 120]. Kuma wadannan Ayoyi ba'a saukar dasuba, a Zamanin Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam domin wasa ko ba’a, A’a an saukar dashi ne, domin wata Manufa me girma, itace: Tabbatarwa ga zuciyar Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasllam da kuma zukatan Muminai dasuke tare dashi.

To D’an Uwa! idan kayi tunani gameda faɗin Allah Madaukakin Sarki: [Sukace: ku k’onashi kuceci gumakanku, idan kun kasance masu aikatawa, se mukace: Yake wuta kizama me sanyi da Aminci ga Ibrahim* se sukayi nufin makirci akanshi se muka sanyasu sune masu Asara] [Sur. Al-Anbiya’i : 68-70] . Abdullahi dan Abbas Allah yakara masa yarda Yace: “Maganar k’arshe da Annabi Ibrahim Yayi da’aka jefashi cikin wuta shine: (Hasbiyal lahu Wani’imal Wakil)”. Ma’ana Allah ya’isar mun kuma madalla da abin dogaro. Shin bakaji wata ma’ana ba, daga ma’anonin tabbatuwa ta shiga cikin ranka – a gaban masu dagawa da Azaba – lokacin da kake karanta wannan K’issa?

Idan kayi tadabburin (tunani akan) Faɗen Allah Madaukakin Sarki a cikin K’issar Annabi Musa: [A lokacin da sukaga tarun runduna, se mutanen Musa sukace: tabbas zasu riskemu * Yace: A’a Lallai ina tareda Ubangiji na, ze shiryar dani] [Sur. Ash Shu’ara’I: 61-62] . Shin bakaji wata ma’ana ba, daga ma’anonin tabbatuwa lokacin haduwa da Azzalumai, dajin tabbatuwa a lokacin tsanani, sanda masu yanke tsammani suketa ihu, a lokacin da kake karanta wannan k’issar?. Haka da zaka bijiro da K’issar mutanen Fir’auna masu Sihiri, Wannan Asali ne me ban sha’awa, na jama’an da suka tabbata akan gaskiya, bayan bayyananta agaresu. Shin bakaga ma’ana me girma daga ma’anonin tabbatuwa wanda yake zama a cikin zuciya a lokacin da Azzalumi yake bada tsoro -wato Fir'auna kenan- Yana cewa: [ Yace: Yanzu zakuyi Imani dashi, tun kafin inyi muku izini, lallai shine babbanku wanda ya karantar daku Sihiri, To Wallahi zan daddatse Hannayenku da kafafuwanku daban daban, kuma Wallahi zan tsireku a kututturen dabino, kuma Wallahi zaku san wanene cikinmu yafi tsananin Azaba kuma tafi wanzuwa ] [Sur. Taha: 71]. Tabbatuwan Muminai Y’an kaɗan, wanda ko kad’an suka ƙi su dawo kan ɓata, kuma suka ce: [ har abada bazamu fifitaka ba akan abinda yazo mana daga Ubangijinmu na gaskiya, kuma shine wanda ya k’agi halittanmu, ka zartar da abinda zaka aikata, kawai zaka zartar da abune a wannan rayuwan ta duniya] [Sur. Taha: 72]. Hakanan K’issar Muminin nan a cikin Suratu Yasin da Muminin Suratu Ali’imrana da Ashabul Ukhdud wato Ma’abota raami da sauransu kusan tabbatuwa kusan shine babban darasin dake cikin dukkansu.

NA HUDU: YIN ADDUA: Yin Addu’a yana daga cikin Siffofin Bayin Allah Muminai shine suna fuskantar Allah, da Addu’a daya Tabbar dasu, suna cewa: ** Ya Ubangijinmu kada ka karkatar da zukatanmu bayan ka shiryar damu. (Rabbana La tuzig ƙulubana ba'ada iz hadaitana) ** Ya Ubangijinmu ka bamu wani irin Hakuri kuma ka tabbatar da diga –digan mu. (Rabbana afrig alaina Sabran) Kuma tunda “ Dukkan Zukatan Y’an Adam suna tsakanin yatsu biyu ne daga yatsukan Ubangiji kamar zuciya ce k’waya d’aya yana juyasu yanda yakeso” Imamu Muslim da Ahmad . Shiyasa Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, yake yawan faɗin: “Ya me jujjuya zukatu ka tabbatar da zuciya ta akan Addininka” Tirmidhi