MARABA DA ZUWA SHAFINMU NA MUSULUNCI

31 Dec 2007

TARE DA MANZAN ALLAH SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM NA (1)

HAIHUWAR MANZAN ALLAH SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM

1. Allah Madaukakin Sarki Yace:. ( Hakika Allah yayi baiwa akan Muminai da ya aiko da manzo daga cikinsu, yana karanta masu Ayoyinsa, kuma yana tsarkakesu, kuma yana karantar dasu Littafi -wato Alk'ur'ani da Hikma -watom Hadisi, duk da sun kasance kafin hakan suna cikin bata a bayyane) S. Al'imaran-164.

2. kuma madaukakin Sarki yace: ( kace masu nifa mutum ne kamanku, anayimini wahayi cewa tabbas mahaliccinku shine ubangiji guda daya) S. kahf-11.

3. An tambayi Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam gameda Yin Azumin Ranar Litinin?

Yace: " wannan rana ce da'aka haifeni a cikinta, kuma a cikinta aka aikoni, kuma a cikinta aka saukar min da Alk'ur'ani" Muslim

4. Hakika an haifi Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam a Ranar Litinin cikin watan Rabi'ul Awwal a Makka, a shekaran Fil- wato Giwa. shekara ta 571 C.E. daga Iyaye biyu sanannu: Mahaifinsa shine ABDULLAHI dan Abdulmutallib, Mahaifiyarsa kuma itace AMINA yar Wahabu, kakansa yarada masa suna MUHAMMAD Sallallahu Alaihi Wasallam, kuma Mahaifinsa ya rasu kafin Haihuwarsa.

5. Lallai Yana daga cikin Abubuwan dasuke wajibi akan Musulmai shine su san darajan wannan Manzo me girma, kuma suyi hukunci da Alkur'ani da'aka saukar masa, kuma su dabi'antu da halayensa kuma su bada kokari wajen kira zuwaga Tauhidi-kadaita Allah- wanda akansa yafara...........................me bin Umarnin Allah Madaukakin Sarki: ( Kace ina kira zuwaga Ubangijina kuma bazana hadashi da kowa ba cikin bauta). Sur.Aljinn-20.

18 Dec 2007

LAYYA

16 Dec 2007

YANKAN LAYYA BA'A GARIN ME LAYYA BA

TAMBAYA: Mu muna zaune a wani Gari, kuma Mahaifiyata da Y'an Uwana suna yanka wani adadi na Layya a kowace shekara, Ni kuma inaso in aikawa da Kawuna da kudin abin Layya na , don yasaya yayi min yankan, saboda halin talauci da suke a ciki, kuma shi kawuna yana zaune a wani gari ne da ban, shin ko zaku bani shawara gameda haka, koko inyi layya na a garin danake zaune, kuma wanne ne yafi falala? tunda ni zan wakilta wani ne da yayi min yankan, kuma bazanga dabban ba yayin da'ake yankata. MAI BADA AMSA: Prof. Dr. Sa'ud bn Abdullah Alfunaisan. Tsohon shugaban Faculty of Shari'ah, Imam Muhammad Bn Sa'ud University Riyadh. RANA: 05-12-1428 A.H. AMSA: Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Tsira da Aminci su Kara tabbata ga Manzan Allah. Bayan Haka: Ya Halarta ka wakilta Kawun ka dayake wani gari da kabashi kudin yasaya kuma yayi maka yanka, saboda ita dai Layya, sunna ce me karfi, wasu kuma sukace wajibi ce ga wanda yake da hali, kuma kallon yankan da kuma cin naman abin layyan, sunna ce ba wajibi ba, musamman kuma tunda Iyalanka zasu yi layyan, kuma abin layya guda daya yana isarma mutum da iyalan gidansa koda suna da yawa, kuma kamar yadda ka bayi bayanin halin da kawunka yake ciki wato yafi iyalanka bukata, saboda haka inka bashi kudin layyan yana wata kasa yayi maka, yahalarta a cikin Shari'a. Allah shine mafi sani.

11 Dec 2007

HAJJI DAI FARKO

Ni Babban ma'aikaci ne kuma me tarbiyya, Alhamdu Lillah Bani da gidana nakaina, ina haya ne, kuma ina da kudin da baze isheni sayen gida ba amma ze ishe ni yin aikin Hajji. shin zan sauke faralin Hajji ne tareda cewa ina haya? shin kuma ya halarta agareni da in jinkirta yin Hajjin har se nase gida, tare da cewa wannan hakan ze dauki shekaru masu yawa? Daga: Shafin: www.islamtoday.com/questions Malami me Amsa: Al'allama Ustaz Dr. Abdullahi bn mahfuuz bn biih, tsohon Ministan ma'aikatan Shari'a ta kasar Mauritania. Rana: 01-12-1428 A.H. Amsa: Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Tsira da aminci su tabbata ga Manzan Allah. bayan haka Wajibine gareka yakai dan'uwa da kaga batar da wajabcin Hajji, domin shi wajibine da baayin jinkiri a cikinsa, kamar yanda da yawa daga cikin Malamai suka tafi akai, to tunda kanada kudi daze ishekan yin aikin Hajji, kuma bazaka bar iyalanka ba a cikin kunci, toyazama dole akanka katafi kayi aikin Hajji kada ka jinkirta shi, domin Hajji wajibi ne, wanda ba'a jinkirta shi, kasmar yanda Imamu Malik da Imamu Ahmad suka tafi akan haka, kuma zance ne me k'arfi a wajen Hanafiyya.

9 Dec 2007

SUMBANTAN KA'ABA?

DAGA: Shafin: www.meshkat.net TAMBAYA: Shin Yana daga cikin Sunnah Sumbantan Ka'aba? MAI BADA AMSA: Sheikh Dr. Abdul-Hayyi Yusuf. Limamin Masallacin Jum'a dake Hayyud dauha, a Khartoum kuma Shugaban Sashin Thaqaful-Islamiyyah a Khartoum University a kasar Sudan. Dukkan Godiya ta tabbata ga Allah Shi kad'ai, kuma Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga wanda babu wani Annabi a bayansa, da Alayensa da Sahabbansa baki daya. Bayan Haka: Abinda yake Sunna dai, Shine sumbantan Hajarul Aswad da Ruknul Yamaani, kuma baya daga cikin Sunnah sumbantan wani abu wanda ba su ba, kamar ka'aba Allah yakara mata, kuma Sahabi Abdullahi dan Abbas Allah yakara masa Yarda, yayi inkari - wato ya nuna kyamarsa ga wanda ya sumbanci wani abu wanda ba Ruknai guda biyu ba- wato wanda aka ambanta-. Allah shine mafi sani.