MARABA DA ZUWA SHAFINMU NA MUSULUNCI

28 Jan 2014

MUTUWA DA KOWA KESO KYAKKYAWAN K'ARSHE

SHIN KO KASAN ALAMOMIN KYAKYAWAN CIKAWA?
Dukkan Musulmi na kwarai yana fatan yayi kyakyawan cikawa a lokacin da ze bar duniy. kuma ana iya ganin alamu da Nassin Hadisan Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya bayyana alamomin Suna dayawa, hakika Malamai Allah yayi masu Rahama sun bibiyesu suka sakamakon karanta Nassoshin dasuka zo akan haka, amma mu anan zamu kawo wasu ne daga cikinsu akwai:
* Furta kalman Shahada a lokacin mutuwa, kuma dalili akan haka shine Hadisi da Hakim ya ruwaito da waninsa daga Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasllam Yace: “Duk wanda karshen maganarsa yazama La ilaha illal lahu ze shiga Aljanna”.
* Mutuwa da Gumi na kwarara akan kumatu, wato yazama a kumatunsa akwai gumi a lokacin mutuwa, Saboda Hadisin da Buraida dan Hasib yaatuwaito cewa: Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasllam Yace: “ Mumini yana Mutuwane da gumi a kumatunsa” Ahmada da Tirmidhi.
* Mutuwa a ranar Jumu’a ko a darenta: Saboda fadin Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasllam Yace: “Babu wani Musulmi daze mutu a ranar Juma’a ko a daren juma’a face Allah ya kareshi daga Azabar Kabari”.
* Yin Shahada a filin Yak’I saboda daukaka Kalmar Allah: ko ya mutu yana yaki saboda Allah ko ya mutu saboda rashin lafiya ta Annoba ko ciwon Ciki, ko ruwa yacishi Kuma dalili akan abubuwan da suka gabata shine Hadisin da Imamu Muslim daga Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasllam Yace: “ Wanene kuka kigawa cikin wanda sukayi Shahada a cikinku? Sukace: Wanda aka kashe saboda Allah shine wanda yayi Shahada, Yace: kenanan masu yin Shahada a cikin Al’ummata yan kad’an ne. se Sukace: To su wanene Ya Manzan Allah? Yace: "wanda aka kashe saboda Allah yayi Shahada, wanda ya mutu akan tafarkin Allah yayi Shahada, wanda ya mutu saboda Annoba yayi Shahada, wanda ya mutu saboda ciwon ciki yayi shahada, da wanda ya mutu saboda ciwon ciki yayi shahada, da wanda Ruwa yaci yayi shahada”.
* Mutuwa saboda Rushewar Gini: Saboda Hadisin da Imamul bukhari da Muslim suka ruwaito Daga manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasllam Yace: “ Wadanda sikayi mutuwan Shahada su biyar ne: “ wanda aka Soka da Mashi, da Me ciwon Ciki, da wanda ruwa ya Nutsa dashi, da wanda Gini ya fad’a ma, da wanda Yayi shahada saboda Allah”.
* Mace ta mutu a lokacin haihuwa saboda d’anta ko ta mutu dashi a ciki, kuma dalili akan haka shine ingantaccen Hadisin da Imamu Ahmad ya ruwaito daga Ubbadatu dan Samit cewa: Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasllam Ya bada labarin masu shahada se ya ambata a cikinsu: “Macen da danta ya kashe ta….. danta ze jawota zuwa Aljanna da cibiyarsa” wato ze da igiya ta ikon Allah wanda ake yanke masa.
* Konewa da wuta : dalilin haka shine Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasllam Ya ambaci adadi na masu shahada se ya ambaci wanda wuta ta kona..........................
* Mutuwa da ciwon rashin lafiya, Annabi Sallallahu Alaihi Wasllam Yabada labarin hakan, cewa Shahada ce.