MARABA DA ZUWA SHAFINMU NA MUSULUNCI

31 Aug 2008

DARUSSAN AZUMI NA (1)

Dasunan Allah Me Rahama Me Jinkai
ME ZAMU KOYA NA DARUSSA A CIKIN MAKARANTAR AZUMIN RAMADAN?
Godiya ta tabbata ga Allah , tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga shugaban halittu , Muhammad Sallallahu Alaihi Wasalam , wanda aka saukarwa da Alkur'ani a cikin watan Ramadan da Iyalan gidansa , masu tsayuwan dararen , da Sahabbansa wadanda suka kasance suna raya dare da Yinin Ramadan da ibada.
Watan Ramadan da irin falalar da Alah yasanya a cikinsa , da abubuwan da'aka shar'anta a cikinsa na ayyukan lada ana daukarsa a matsayin Makaranta ce da Mumini ze samu mafi daukakan ilimomi , daga ciki akwai mafi girman sani , ta yanda koda Ramadana ya wuce – wato yakare kenan zebar wadansu alamomi ga Mumini , saboda ribatuwa dayayi da wannan watan.
TO YAZAMUYI MUSANYA RAMADAN YAZAMA MAKARANTA GA RAYUKANMU?gasu kamar haka:-
NA FARKO:- JIN TSORON ALLAH:
Azumin Watan Ramadan yana daga cikin mafi girman dalilan dake tsarkake Rai , duk wanda ya Azumce shi yana me Imani dashi da kwadayin lada Ransa zata tsarkaka , tayi danshi , kuma ta kubuta daga abubuwan da'aka haramta da Sabo. To Wanke Rai da tsarkaketa , dayane daga cikin mafiya girman manufofin Azumi. Allah subhanahu Wata'ala Yace:- ( Yaku Wadanda sukayi Imani , an wajabta maku yin Azumi , kamar yadda aka wajabta akan wadanda suka gabace ku , domin kusami takawa –wato tsoron Allah-) [Sur. Baqarah- 183].
Shaikh Sa'ady a cikin Tafsirinsa Yace: " Ambaton Allah ga Azumi fa'ida ce me girma wacce take kunshe cikin Fa'idodi masu yawa , fadansa ( domin kusami jin tsoron Allah)
Ma'anarsa Azumin yazama hanyace agareku wajen samun jin tsoron Allah , kuma domin ku kasance a cikin masu jin tsoron Allah ta dalilin Azumin , saboda haka jin tsoron Allah sunane daya kunshi dukkan abinda Allah yakeso , kuma ya yarda dashi , na aikata abubuwan da Allah da Manzansa suka wajabta da barin dukkan abinda Allah da Manzansa suke ki , saboda haka Azumi hanyace mafi girma dan cimma wannan gaya me girma, wacce take kai bawa zuwa ga jin dadi da tsira.
Lallai me Azumi yana samun kusanci zuwa ga Allah da barin abinda Ransa takeso na abinci abin Sha da makamantansu , gabatar da Son Allah akan Sansa ga kansa.
Sannan Jin tsoron Allah shine Farkon darasi da me Azumi ze samu saboda haka dole ne yakiyaye hakan , Mumini me Azumi me neman lada baya sanya burinsa da himmarsa wajen samun jin tsoron Allah a cikin kwanakin Ramadana kadai , A'a niyyarsa tafi haka , shi dai yana yin Azumin Ramadana ne domin ya sabunta alkawari tsakaninsa da Alah , Alkawarin yin bauta tsarkakka ga Allah , wanda gabobinsa suna Azumin da kamewa daga sabon da Rai takeyi , kuma ya sabunta Alkawari da tuba , kuma ya karfafa himmarsa akan cigaba da yiwa Allah biyayya har zuwa mutuwa , To wannan shine wanda ya fahimci manufar Ramadan , wanda be takaita Jin tsoron Allah dayakeyi akan watan Ramadana kadai ba , A'a Jin tsoron Allah na cigaba har abada.