MARABA DA ZUWA SHAFINMU NA MUSULUNCI

29 Nov 2007

ABUBUWAN HANI A CIKIN HAJJI

ABUBUWAN DA AKA HARAMTASU GA MAHAJJACI

Duk wanda yayi Harama da Hajji ko Umurah an haramta masa, abubuwan da suke zuwa: 1.Rufe kai ga na miji, domin haramarsa itace bude kai, haka kuma Rufe fuska da Hannaye ga mace, domin haramarta itace budesu, sedai idan zata wuce maza, to seta rufe fuska. Kuma idan daya daga cikinsu yarasu, to za’a rufeshi a cikin haraminsa, se abude fuskar maace, kuma a bude kan na miji, kuma baza’a samasa turare ba.

2. Aske gashin kai ga na miji.

3.Yanke kumba.

4. Sanya Turare, sedai abinda yake a tufafinsa, wanda yayi harami dashi to babu laifi akansa.

5.Sanya tufafi dunkakke.

6. yin Jima’I da abubuwan dasuke haifar dayinsa.

7. Yin farautan wani abu, ko temaka ma meyin hakan, ko cin abinda akayi farautarsa.

8. Yayi tad’i wato neman aure, ko daura masa aure, ko aurarwa waninsa, ko ya halarci daurin auren waninsa.

WAR-WARE AIKIN HAJJI KARAMA DA BABBA

Mahajjaci yanada war-wara guda biyu: Karama shine bayan jifan jamratul ak’aba –wato shedan babba- a ranar Idi kenan, to daga nan komai ya halatta ga mahajjaci hatta saduwa da Iyali. da kuma War-wara babba, wanda yake bayan dawafin Ifada.

FIDIYA GA WANDA YA AIKATA ABINDA AKA HARAMTA

Duk wanda ya aikata daya daga cikin abubuwa guda biyar na farko da’aka haramta masa, da gangan –wato-yana sane bada mantuwa ba- to akwai fidiya akansa, kuma yanada zabi a cikin hakan, kodai ya yanka dabba, ko ya ciyarda Miskinai guda shida, ko yayi Azumin kwana uku (3) a duk inda yaso. Saboda faden Manzan Allah Sallalahu Alaihi Wasallam ga Ka’ab dan Ujratu Allah yakara masa yarda: …………………………………………………

AIKIN HAJJI

Menene Ma'anar Hajji? Hajji a harshen larabci ma'anarsa itace nufi ko aiki da yake zuwa lokaci zuwa lokaci. Amma a musulunci, idan akace hajji shine Nufin dakin Allah me alfarma domin aiwatar da wasu ayyuka kebantattu da Alalh madaukakin sarki ya ambata acikin littafinsa kuma Hadisai sukayi bayani akansu.

HUKUNCIN AIKIN HAJJI

Yin aikinHajji wajibine akan kowani musulmi na miji da musulma mace dasuke da iko. Kuma aikin Hajji ya tabbata acikin Littafi da Hadisi da Ijma'i.

Daga cikin Littafi : Allah madaukakin Sarki Yace: ( kuma lallai Allah ya wajabta wa mutane yin Hajjin dakinsa ga wanda yasami iko,kuma duk wanda ya kafirce to lallai Allah mawadaci ne ga Halittu.) Sur. Al'imrana

Daga Hadisi : Abdullahi dan Umar ya ruwaito Hadisi daga Mnazan ALLAH Sallalllahu Alaihi Wasallam yace: ( An gina musulunci ne akan abubuwa guda biyar : Shaidawa babu abin bautawa da can canta se Allah kuma Annabi Muhammadu Manzan Allah ne,Tsayar da Sllah, Bayar da Zakkah, Yin Hajji da kuma Azumin Watan Ramadana) Bukhari da muslim.

Daga Ijmaa'I : Dukkan Musulmai sun hadu akan wajabcinshi kuma dayane daga cikin rukunnan musulunci, kuma abune da kowa yasanshi acikin Addini, kuma duk wanda yyi musunsa to ya kafirta kuma yaayi rudda daga musulunci, haka kuma malamai sun hadu akan cewa aikin Hajji baya wajaba face sau d'aya a rayuwar mutum se dai idan mutum musulmi yayi bakancensa wato alwashi to yazama dole ya cika alwashinsa, amma duk abinda yayi bayan wannan to neman lada ne kawai.

Abdullhi dan Abbabs Allah yakara yarda agareshi yace Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yayi mana Khud'uba, se yace: (Yaku mautane Allah ya wajabta aikin Hajji akanku ) se Ak'ra'a bin Habis yace "Shin kowace shekarane ya manzan Allah? Se yayi shiru har se da ya maiamaita hakan sau Uku, sannan Manzan Allah Sallallahu Alaihin Wasalllam yace : ( da'ace nace E da yazama wajibi, kuma da dayazama wajibi bazaku yiba kuma bazku iyaba, Hajji sau dayane duk wanda yakara to neman ladane ) Ahmad, Abu dawud da Nasa'i.

FALALAR AIKIN HAJJI

Allah ya kwadaitar damu yin aikin hajji kuma ya bayyana d'umbin ladar da za'a samu a sakamakon hakan hadisan dasuke zuwa zasu bayyana haka:

Fadin Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam : ( Duk wanda yayi Hajji, be yi rafasu ba -wato Jima'i a cikinsaba- kuma beyi fasikanciba –sab'on Allah- ze koma mara laifi kamar randa mahaifiyarsa ta haifeshi ) Bukhari da Muslim.

Fadin Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam : (Yin aikin Umurah zuwa Umurah ana kankare zunubbai dake tsakaninsu, shiko aikin Hajji karbabbe baya da sakamako se Aljanna.) Bukhari da muslim.

Fadin Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam : yayinda aka tambayeshi gameda mafificin ayyuka se yace " Imani da Allah da manzansa" akace seme kuma? Yace "se jihadi dan daukaka kalmar Allah" akace se me kuma? Yace" se aikin Hajji karbabbe". Bukhari da Muslim.

Fadin Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam………………..

SHARUDDAN WAJABCIN HAJJI

Seda sharudda masu zuwa hajji yake zama wajibi:

1. Musulunci

2. Balaga

3. Hankali: wato yakasance me hankali domin Hajji baya wajaba akan mahaukaci.

4. Y'anci: wato yazama d'a,domin hajji baya zama wajibi akan bawa. Dalilan wadannan sun gabata a cikin rukunin Azumi.

5. Samun iko: kamar yadda Allah madaukakin Sarki yace ( kuma lallai Allah ya wajabta wa mutane yin Hajjin dakinsa ga wanda yasami iko….) Sur. al'imrana -97.

RUKUNNAN HAJJI

Rukunnan Hajji guda hudune(4): Yin harama, Tsayuwa a Arafah, Yin d'awafi da Yin Sa'ayi kuma rashin yin daya daga cikin wadannan yana bata hajji.

Na Farko: Yin Harama: shine Niyyan shiga cikin aikin hajji ko Umurah kuma niyyan takasance a ntareda lokacin da mutum ze cire tufafinsa da talbiyya. Kuma harama tana da nau'o'i uku: Tamattu'I, Qiraani da Ifraadi.

Tamattu'I : ma'anarsa shine musulmi yayi harama da Umara ita kadai a cikin watannain Hajji, idan ya 'isa makka se yayi dawafi yayi sa'ayin umura yayi k'wal kwabo ko saisaye, idan ranar tarwiya wato ranar takwas ga zulhajji, se yayi harama da Hajji shi kad'ai yayi dukkan ayyukan Hajji ya yi hadayan Tamattu'I da yayi idan shi ba mazaunin garin makka ne ba.

Qiiraani: shine yayi harama da Umara da Hajji a tare daga mikaati ko kuma yayi harama da Umara a farko se yashigar da aikin hajji a ciki kafin yayi dawafi kuma ze cigaba da kasancewa a cikin haraminsa har zuwa lokacin da zeyi jifan jamrah a ranar idi se ya aske kansa kuma yayi hadaya kamar me tamattu'i.

Ifraadi : shine yayi harama da hajji kadai, ya cigaba da zama a cikin haraminsa har zuwa lokacin da ze jefi jamrah ranar idi sannan ya aske kansa kuma babu fidya akansa wato babu jini akan haka.

28 Nov 2007

FATAWA AKAN MAFARKI (2)

DAGA: Shafin: www.islamtoday.com Menene Bambanci tsakanin Wankan Janaba da Wankan tsabta? wajen isarwarsu daga alwala ko rashinta? kuma shin yin Alwala sharadi ce gameda wankan tsabta? dakuma wajen yin niyya, Allah yasaka maku da Alkhairi. Mai bada Amsa: Dr. Sulaiman bin Wa'il Attuwaijiri, Mamba a kwamitin malamai na Jami'ar Ummul Qura dake makkah. Rana: 27-6-1424 A.H. Amsa: Wankan Janaba, wankane dayake dauke Hadasi babba, ita kuma Alwala tana dauke hadasi ne wanda yake karami, shi kuma wanka na tsabta, ba ya dauke wani hadasi, to da mutum zeyi niyyan wanka, wato bana janaba ba, kawai yayi wankan tsabta ne ko wankan juma'a, se yayi nufin dauke hadasi karami dashi wato alwala, to be isar masa ba, domin a wankan babu nufin dauke hadasi a cikinsa, Allah madaukakin Sarki kuma yana cewa "kuma idan kun kasance masu janaba to kuyi tsarki" to alwala tana shiga cikin wankan janaba wajen dauke hadasi, se hadasi karani ya shiga cikin hadasi babba, wajen daukewa da abinda ze halarta sallah, amma shi kuma wanka na tsabta, badauke hadasi yakeyi ba saboda haka be idarwa gameda alwala, myazama dole yayi alwala da farillanta da jerantawa a gabbai. Allah dhine mafi sani.

FATAWA AKAN MAFARKI (1)

Menene Ma'anar Mafarki kuma Yaya Yake? Daga Shafin: www.islamtoday.net/question Mai Amsa Tambaya: Al-allamah Abdurrahman bn Abdullahi Al-ajlan Malami a haramin Makkah. Rana: 15-12-1422 A.H Amsa: Mafarki Shine mutum yagansa yanayin Jima'i da wata mace, to idan ya fitar da maniyyi a wannan lokaci to wanka ya wajaba akansa, idan kuma bai fitar da maniyyi ba, wankan bezama dole akansa ba, saboda fadin Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam "Ruwa yana wajaba ne -wato yin wankan janaba- saboda fitar ruwa -wato maniyyi" Muslim ya ruwaitoshi lambar hadisi na 343 daga hadisin Abu Sa'idil Khuduri Allah yakara masa Yarda.

27 Nov 2007

FATAWA AKAN TABARRUKI

Menene Hukuncin Tabarruki (Neman Albarka) da duk wani abu da yashafi Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, a Lokacin dayake da rai, da bayan mutuwarsa, da tabarrukin da Sahabbai sukayi da Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam a lokacin rayuwarsa, kuma shin hakan ya tabbata a bayan rasuwarsa? kuma naji cewa Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yaba wani bargonsa, kuma a binne wani dashi a bayan mutuwarsa? kuma shin yatabata cewa Abdullahi dan Umar yayi tabarruki da mimbarin Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam? kuma meye ra'ayinku gameda wanda yake cewa yanada gashin Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam?.
Malami da ya amsa: Ustaz Dr. Khalid almushaiqih
Rana: Alhamis 30 Rajab 1427 A.H
Lambar Fatawa: 16619.
Daga: shafin www.almoslim.net
Dukkan yabo da godiya sun tabata ga Allah Mahaliccin Bayi, tsira da Amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad da Alayensa da Sahabansa gabaki daya. bayan haka:
Yin Tabarruki da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam a lokacin da yake da rai, ya kunshi nau'i guda biyu na Albarka, Albarka tashi da kansa da Albarka ta ma'ana.
Amma neman albarka tashi ta kansa: To Sahabai Allah yakara Yarda agaresu, sun kasance suna yin tabarruki da Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, saboda Allah Subhanahu Wata'ala yasanya albarka agaresa, kamar yanda hakan yazo a cikin Hadisin Bukhari da Muslim da waninsu, cewa sunayin tabarruki da Gashinsa da Yawunsa da kakinsa da guminsa da tufafinsa da sauransu. Nau'i na biyu kuma shine: yin Tabarruki na Ma'ana, Annabai Sallallahu Alaihi Wasalllam, Shine mafi girman dalili ko sababi ga al'ummarsa na samun Albarka ta hanyar karantarda su da shiryar dasu da fitar dasu daga duhu zuwa gas haske. to amma bayan wafatinsa, to Albarka ta ma'ana ta yanke, sedai abinda aka ruwaito daga wasu daga cikin Sahabbai Allah yakara masu yarda, cewa sun kasance sun kiyaye wasu daga cikin abubuwa na Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam kuma sunayin Tabarruki dasu kamar yadda yazo a cikin Sahih Abukhari, daga Ummu Salamah Allah yakara yarda agareta, tanada abun wuya na azurfa ta kiyaye gashin Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam a ciki, to irin wadannan alamomi ko abubuwa, sahabbai sun kasance, sun kiyiyesu. To amma a Yau: irin abinda shuwagabannin Sufaye suke ik'irari da y'an damfara na cewa sunanan da wani sashi na gashin Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, ko tufafinsa ko makamancin haka, duk k'arerayine da basu da wata kamshin gaskiya, saboda basu da wani dalili -wato hujja akan hakan- ingantatta a cikin Shari'a ta sanadi, to saboda haka babu wani abinda yarage face, Albarka ta ma'ana, ta neman Albarka da abubuwan daya fuskantar, da abubuwan dayayi umarni dasu da abubuwan dayayi hani dasu da tsayuwa akan Sunnarsa da nisantar Sab'a masa. kuma ga Allah muke neman dacewa.

1 Nov 2007

Jana'izar Malam Ja'afar

Wannan Itace Jana'izar Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam Allah Yayi masa Rahama Amin.