MARABA DA ZUWA SHAFINMU NA MUSULUNCI

23 Sept 2008

I'ITIKAFI

Dasunan Allah mai Rahama Mai Jinkai

Shine lazimtan masallaci da zama cikinsa da niyyan samun kusanci zuwa ga Allah. kuma malamai sunyi ittifak'I -wato sun hadu- akan cewa itikafi an shar'antashi kuma mustahabbi ne.

Tunatarwa: wasu mutane na kuskure ta yanda suke daukan cewa Itikafi, yakebanci manzan Allah ne Sallalahu Alaihi Wasallam shi kadai, wasu kuma suce hadisin Itikafi an shafe shi, wasu kuma suna dauka cewa Itikafi na dattawane ko akasin hakan, to duk wadannan kurakurai ne ba'a sha. Nana A'isha Allah yakara yarda agareta tace: (Lallai manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yakasance yanayin Itikafi a cikin goma na K'arshe na Ramadan har Allah yadauki ransa, sannan matansa sukayi Itikafi a bayansa) Bukhari. Ibn Hjar yace (Ba'a shafe hadisin ba kuma baya cikin abubuwan da suka kebanci ManzanAllah Sallallahu Alaihi Wasallam)fathul baari 4/272.

HUKUNCIN ITIKAFI

Mafi yawan malamai sun tafi akan cewa mustahabbi ne.

Imamu Malik Yace: (Nayi tunani akan al'amarin Itikafi, da abinda yazo akansa, da yanda musulmai suka barshi, tareda cewa manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, be kasance yabarshi ba, se naga cewa sun barshi ne saboda yanada wahala akansu.)

Imam Azzuhri Yace: (akwai mamaki a Al'amarin musulmi! Sun bar Itikafi, tareda cewa Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, be barshi ba tunda yazo Madinah , har Allah madaukakin Sarki yadauka ransa.)

SHARUDDAN ITIKAFI

1. MUSULUNCI: baya inganta ga wanda ba musulmi ba.

2. HANKALI: mahaukaci baya itikafi, saboda koda ibada ta wajibi bata zama dole akansu ba, andaga alkalami akansu.

3. NIYYA: sharad'I ce ga dukkan ibadodi, kuma duk aikmin da babu niyya a cikinsa ba karbabbe bane.

4. MASALLACI: ga namiji dolene yayi a masallaci, amma mace kuma anyi sabani akanta, Malam SUHNUNU Yace: (nace ma ibnul K'asim: menene zancen Imamu Malik gameda Itikafin mace tayi amasallacin jama'a? se yace Na'am, yace: a zancen Malik tayi Itikafi a masallacin gidanta? Se yace: Hakan baya burgeni, ana itikafi ne a masallacin da'aka yishi dan Allah.) Mudawwana 1/295.

Sheikh Aminul Hajj yace: (amma yafi rinjayen dalili awurina shine mace tayi Itikafinta a gidanta, wato wurin da takebance shi tana sallah a cikinsa.

5. AZUMI: wasu daga cikin malamai sukace kada mutum yayi itikafi face yaname Azumi, an tambayi Ibnul K'asim: (shin anayin itikafi batare da azumi ba a cikin zancen Malik? Se yace: ba'ayi se da Azumi. Wasu kuma sukace anayi koda mutum beyi Azumi ba, Sukace wannan shine ra'ayi mafi rinjayen dalili, saboda Hadisi Umar ingantacce da Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya Umarce shi da yayi itikafi yayin da yace masa yayi alwashin yin hakan a jahiliyya, kuma be ce masa yayi Azumi ba.

6. IZINI: dolene se miji yayi wa matarsa izini ko abinda ya mallaka na bawa ko baiwa, miji mace yana gida ne ko yayi tafiya dole tanemi izininsa, kuma idan yayi mata izini, to be kamata ya hanata ba kuma.

RUKUNNAN ITIKAFI

1. Zama a cikin Masallaci. 2. Nisantan Jima'I da abubuwan da zasu iya kaishi yin hakan. 3. Nisantar manyan laifuka. 4. Musulunci. 5. Hankali. 6. Tsarki daga Haila. Itikafi yana baci saboda rashin daya daga cikin wadannan.

ABUBUWAN DASUKE BATA ITIKAFI

1. FITA DAGA MASALLACI: baya halasta fita daga masallaci, In banda fita saboda: dan Biyan bukata kamar fitsari ko bayan gari, wankan janaba da na jumu'ah, cin abinci ko abin sha idan be iya ci ko sha a wurin da yake itikafi, idan yaji tsoron wuta ko sata kom rushewan gini, in aka fitar da shi da karfi, idan mace tayi haila da sharadin ta dawo da tayi tsarki, idan mijin mace yarasu ko yasake ta zata fita a mafi rinjayen zancen malamai biyu wasu sukace zata cigaba har seta kammala, fita saboda yin Umara, fita da mantuwa, idan yayi hauka ko suma.

2. YIN JIMA'I: saboda Allah yace: (kuma kada ku sadu dasu, alhalin kuna masu Itikafi a cikin masallatai…) Sur.Baqarah-186. haka sun bantan mace da sha'awa.

3. YIN RIDDA:wato fita daga musulunci

4. YIN MANYAN LAIFUKA: kamar yin zina da sata acikin itikafi, wanda mutane suna sakaci da daukan abin wani ko da kadan kuwa se a kiyaye.

5. YIN HAUKA KO SUMA: yana bata itikafi se dai idan yasami lafiya ko ya farfad'o to se yacigaba.

6. HAILA: idan mace tayi haila itikafinta ya baci, amma idan tayi tsarki se ta cigaba, na bayan be baciba.

ABUBUWAN DA BA'ASO GAME ITIKAFI

Ba'aso me itikafi ya shagaltu da abinda ba ambaton Allah ba, da kuma abinda ba dolene ba.

1. jayayya. 2. zagi damaganganun banza. 3. Yin giiba da Annamimanci. 4. Kallon abinda yake haramun. 5. Rashin yin magana gaba daya tun daga safe har dare da sunan bauta.

Tunatarwa: wasu daga cikin daliban ilimi se kaga suna zuwa itikafi da wasu littafai na karatunsu suna yin muraja'a, ba haramun bane amma kamata yayi tunda kwanakine yan kadan a cikin shekara, meze sa bazakayi hakuriba, sauran kwanakin shekara kayi acikinsu.

ABUBUWAN DASUKA HALASTA GAME ITIKAFI

1. Yin wanka da canza kaya, da sanya kayan da yakeso.

2. Cin Abinci da Shan Abin Sha a cikin masallaci.

3. Yin magan da yan uwa, amma ba'ason yawaita surutu da mutane.

4.Ya nemi Aure ko a daura masa Aure.

5. Yin Aski da yanke Farce.

6. Sanya turare.

ABUBUWAN DA SUKE MUSTAHABBI GA ME ITIKAFI

1. Mustahabbi ne ga me itikafi, yakafa tanti da ze kangeshi daga jama'a, inbe samu ba se ya lazimce wurin da babu jama'a ta yanda baze barshi ba seda larura.

2. kiyaye yin Sallah cikin jama'a, da nafiloli.

3. Yawan karatun alk'ur'ani, da rashin shagaltuwa da abinda ba ruwa.

4. Yawan ambaton Allah, zikiri, da tasbihi.

5. Yin azumi a cikin wantan da ba ramadan, ga wanda zeyi itikafi da rana.

6. Yawan yin kokari wajen d'a'a.

MAFI KARANCIN ITIKAFI DA MAFI YAWANSA

Itikafin neman lada baya da kad'an ko mafi yawa, se dai wanda yayi Itikafi a goman k'arshe na Azumin kada ya fita se idan anga watan Sallah wato Shawwal, malamai sun hadu akan cewa baya da mafi yawa, amma sunyi maganganu akan karancinsa, wasu sukace mafi karancinsa Sa'a, wasu sukace Yini daya da dare, wasu sukace kwana goma.

Imamul k'urtabi yace: ( mafi karancin itikafi a wajen Malik, da Abu Hanifa, dare da yini….)

YAUSHE AKE SHIGA ITIKAFI KUMA YAUSHE AKE FITA

A. Shiga wajen itikafi:akwai zancen malamai guda biyu:

1. Shiga bayan sallar Asubahin ranar Ashirin da d'aya na Ramadan, saboda hadisin Nana A'isha Allah yakara mata yarda tace: (Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam idan ze shiga itikafi yana yin sallar Asubahi, sannan se yashiga wurin itikafinsa) Bukhari. kuma wannan shine mafi rinjayen dalili. Kuma mazhabinAhmad da Laith da Ishak'.

2. Shiga kafin rana r daren Ashirin da d'aya ta fad'i, wannan shine mazhabin Malamai hud'u

B. Fita daga itikafi: Ana fita daga wurin itikafi bayan ganin watan sallah, wasu kuma sukace mustahabbine ya bari har yayi sallar idi sannan ya tafi.

SIRRIN DA YAKE CIKIN I'ITIKAFI

Bauta tana da sirruka da hikimomi masu yawa, saboda ayyuka gaba daya, makewayansu itace Zuciya, kamar yanda Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Yace (..Kusaurara! lallai acikin jiki akwai wata tsoka wanda idan ta gyaru, to dukkan sauran jiki ya gyaru, kuma idan ta bace, to dukkan Sauran jiki ya baci, ku saurara! Itace zuciya.) Bukhari da Muslim.

To in muka duba zamuga cewa mafi yawan abubuwan da suke bata zuciya, sune sha'awan cin abinci da abin sha da saduwa da Iyali da Zancen da ba na dole ba, da barcin da ba na dole ba, da abokai da basu da wata fa'ida da sauran abubuwa dasuke kawar da zuciya daga yin abinda yake biyayya ne ga Allah, se Allah ya Shar'anta wasu abubuwa na lada da zasukare zuciya daga rud'ani da shagaltuwa daga ambaton Allah, kamar Azumi wanda yake hana mutum cin abinci da abin Sha da Saduwa da Iyali da rana. To wannan hanuwan daga wadannan abubuwan jin dadi, shine yake karfafa alak'a tsakanin mutum da Ubangijinsa, da fuskantar dashi ga Lahira, kena Azumi garkuwa ce datake kare zuciya daga abubuwan sha'awa da suke kawar da mutum daga yin biyayya ga Allah, duk da hanine wanda yake matsakaici saboda an halasta wa mutum wadannan abubuwa a cikin dare.

To haka shima Itikafi yanada Sirri me girma, shine Kare mutum daga yawan cakud'a da jama'a, da yawan magana, saboda me Itikafi yana shagaltuwane da karatun Alk'ur'ani da Tsayuwa –wato yin sallah- da Zikiri da yawan yin Addu'a da makamantansu, haka kuma akwai kariya daga yawan barci, tunda yazo ibada ne ba barci ba, to wadannan abubuwa barinsu shike kara sa zuciya ta fuskanci Allah.

ABUBUWAN TUNATARWA

* Wasu daga cikin malamai sun tafi akan cewa ba'ayin Itikafi se a masallatai guda Uku kamar yadda yazo a cikin Hadisi, na hani akan yin Itikafi a masallatan da basuba, manzan Allah Sallalahu Alaihi Waasallam yace (Babu Itikafi face a masallatai guda uku) imamu Tahawi. -Wato masallacin Harami wato Ka'abah da masallacin Madinah da masallacin Aqsa wato Kudus-, Malamai suka fassara shi da cewa hani ne na yin alwashin yin Itikafi a wani masallaci da tafiya zuwa gareshi saboda hakan se a wadannan masallatan kadai ya halatta, ayi hakan saboda duk malaman mazhabobi Hud'u sun hadu akan cewa ya halatta ayi a kowani masallacin Juma'a.

* wasu sukan bar ayyukansu na wajibi saboda suyi Itikafi, to yin hakan kuskure ne saboda shi Itikafi sunna ce, saboda haka ba'a barin abinda yake wajibi saboda Sunnah.

Ya Allah Ka Karba mana dukkan Ayyukanmu a cikin Watan Ramadana kasa Muna cikin Bayinka Yantattu dag Wuta kuma kadatarmu da daren Lailatul K'adari. Amiin

15 Sept 2008

SADUWA DA MATA CIKIN HAILA

SADUWA DA MATA CIKIN HAILA

Allah Madaukakin Sarki Yace: ( Kuma Suna tanbayarka game da Haila , Kace kazanta ne , Ku Nisanci Mata a cikin Haila , kuma jada ku kusance su har se sunyi tsarki) [Suratul Baqarah - 222].

Saboda haka baya halatta wato Haramun ne Mutum ya kusanci matarsa har se tayi wanka bayan tsarki , saboda Fadin Allah Madaukakin Sarki: (To idan Sunyi tsarki Se kuzo masu ta inda Allah Ya Umarce ku…)[Suratul Baqarah - 222].

Kuma abinda ke nuna munin wannan Laifi Shine Hadisin da Abu Hurairah Yace: Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Yace: (Duk Wanda yazo ma me Haila , ko yazo ma mace ta bayanta , ko yaje wajen Boka , to ya kafirta daga abinda aka Saukar wa Muhammad) [ Imamu Tirmidhi-Vol.1- 243].

Ma’ana wanda ya sadu da matarsa alhali tana cikin Haila , ko ya sadu da ita ta wurin bayan gidanta. To duk wanda ya aikata hakan da kus – kure , bada gan – gan ba , alhali be sani ba , babu komai akansa , wanda kuma ya aikata hakan dagan - ganci yana sane , To zeyi kaffara a daya daga cikin zantukan Malamai wanda sukace hadisin kaffara ya inganta , shine yayi sadaka da Dinar wato Zinare ko rabin Zinare , Wasu sukace yanada zabi cikinsu wato kodai ya bada Zinare ko rabinsa , Wasu Malaman Sukace: Idan yazo mata a lokacin da ta fara Haila to ze bada Zinare cikakke , idan kuma a karshen Hailan yazo mata wato lokacin da jinin ya ragu ko kafin tayi wankan Haila to ze bayar da rabin Zinare. Zinare cikakke kuma ana kwatantashi da 4.25gram ko da kudin da ake sayar dashi. Sannan abinda Malamai sukace shine dai – dai shine Zance da’akace yanada zabi tsakanin zinare ko rabinsa.

31 Aug 2008

DARUSSAN AZUMI NA (1)

Dasunan Allah Me Rahama Me Jinkai
ME ZAMU KOYA NA DARUSSA A CIKIN MAKARANTAR AZUMIN RAMADAN?
Godiya ta tabbata ga Allah , tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga shugaban halittu , Muhammad Sallallahu Alaihi Wasalam , wanda aka saukarwa da Alkur'ani a cikin watan Ramadan da Iyalan gidansa , masu tsayuwan dararen , da Sahabbansa wadanda suka kasance suna raya dare da Yinin Ramadan da ibada.
Watan Ramadan da irin falalar da Alah yasanya a cikinsa , da abubuwan da'aka shar'anta a cikinsa na ayyukan lada ana daukarsa a matsayin Makaranta ce da Mumini ze samu mafi daukakan ilimomi , daga ciki akwai mafi girman sani , ta yanda koda Ramadana ya wuce – wato yakare kenan zebar wadansu alamomi ga Mumini , saboda ribatuwa dayayi da wannan watan.
TO YAZAMUYI MUSANYA RAMADAN YAZAMA MAKARANTA GA RAYUKANMU?gasu kamar haka:-
NA FARKO:- JIN TSORON ALLAH:
Azumin Watan Ramadan yana daga cikin mafi girman dalilan dake tsarkake Rai , duk wanda ya Azumce shi yana me Imani dashi da kwadayin lada Ransa zata tsarkaka , tayi danshi , kuma ta kubuta daga abubuwan da'aka haramta da Sabo. To Wanke Rai da tsarkaketa , dayane daga cikin mafiya girman manufofin Azumi. Allah subhanahu Wata'ala Yace:- ( Yaku Wadanda sukayi Imani , an wajabta maku yin Azumi , kamar yadda aka wajabta akan wadanda suka gabace ku , domin kusami takawa –wato tsoron Allah-) [Sur. Baqarah- 183].
Shaikh Sa'ady a cikin Tafsirinsa Yace: " Ambaton Allah ga Azumi fa'ida ce me girma wacce take kunshe cikin Fa'idodi masu yawa , fadansa ( domin kusami jin tsoron Allah)
Ma'anarsa Azumin yazama hanyace agareku wajen samun jin tsoron Allah , kuma domin ku kasance a cikin masu jin tsoron Allah ta dalilin Azumin , saboda haka jin tsoron Allah sunane daya kunshi dukkan abinda Allah yakeso , kuma ya yarda dashi , na aikata abubuwan da Allah da Manzansa suka wajabta da barin dukkan abinda Allah da Manzansa suke ki , saboda haka Azumi hanyace mafi girma dan cimma wannan gaya me girma, wacce take kai bawa zuwa ga jin dadi da tsira.
Lallai me Azumi yana samun kusanci zuwa ga Allah da barin abinda Ransa takeso na abinci abin Sha da makamantansu , gabatar da Son Allah akan Sansa ga kansa.
Sannan Jin tsoron Allah shine Farkon darasi da me Azumi ze samu saboda haka dole ne yakiyaye hakan , Mumini me Azumi me neman lada baya sanya burinsa da himmarsa wajen samun jin tsoron Allah a cikin kwanakin Ramadana kadai , A'a niyyarsa tafi haka , shi dai yana yin Azumin Ramadana ne domin ya sabunta alkawari tsakaninsa da Alah , Alkawarin yin bauta tsarkakka ga Allah , wanda gabobinsa suna Azumin da kamewa daga sabon da Rai takeyi , kuma ya sabunta Alkawari da tuba , kuma ya karfafa himmarsa akan cigaba da yiwa Allah biyayya har zuwa mutuwa , To wannan shine wanda ya fahimci manufar Ramadan , wanda be takaita Jin tsoron Allah dayakeyi akan watan Ramadana kadai ba , A'a Jin tsoron Allah na cigaba har abada.

20 Jul 2008

SIFFAR BARCIN MANZAN ALLAH SALLALLAHU WASALLALAM

SIFFAR BARCIN MANZAN ALLAH SALLALLAHU WASALLALAM

  • Ya kasance yana Barci a Farkon dare, ya raya karshensa – wato yanayin Sallah a cikinsa kenan- Bukhari da Muslim.

Ø Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam Ya Kasance idan ya hau kan shinfidarsa zeyi Barci yana cewa : “ Bismikallahumma Amutu Wa’ahyaa” (Ma’ana Da sunanka Ubangiji, nake Mutuwa kuma nake Rayuwa. Mutuwa = Yin barci , Rayuwa = Farkawa daga barci) kuma idan ya farka daga barci yana cewa “ Alhamdu lil lahil ladhi Ahyaana ba’ada ma Amaatana Wa ilaihin nushur” ( Ma’ana Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Wanda ya Rayamu bayan ya kashe mu, kuma gareshi tashi yake) Muslim.

Ø Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Ya Kasance idan ze kwanta barci yana sanya tafin Hannunsa na dama kar-kashin kuncinsa na dama se Yace: “Rabbi Qini azabaka Yauma tab’athu ibadika” (Ma’ana Ya ubangiji ka tsareni daga Azabarka ranar da zaka tashi bayinka –wato ranar Lahira kenan) Tirmidhi .

Ø Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam Ya Kasance a kowani dare idan ze kwanta yana hada tafukan Hannayensa se ya huresu Ya karanta (Kulhuwallahu Ahad) da (Kul’a’uzu birabbil Falaq) da (Kul’a’uzu bi rabbin Nas), sannan ya shafama inda ya sauwaka a jikinsa, yana farawa da kansa se fuskarsa da barin gaba na jikinsa, yana yin hakan sau uku. Bukhari da Muslim.

Ø Ya Kasance yana barci a kan matashin kai (pillow) na Fata cikinsa an cikashi da gashin bishiyar dabino Ahmad.

Ø Shimfidar da Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Ya Kasance yana barci akanta ta Fata ce da aka cika da gashin bishiyar dabino Muslim.

Ø Nana Aisha Allah ya kara Yarda agareta tace Ya Manzan Allah Shin kana barci ne kafin kayi Sallar Witri? Se Yace: “ Yake Aisha: Idanuwana suna Barci amma Zuciya ta bata Barci” Bukhari da Muslim.

1 May 2008

NA UKU (3)

NA BIYAR: AMBATON ALLAH (WATO YIN ZIKIRI)

Ambaton Allah yana daga mafi girman dalili na samun Tabbatuwa.

Kayi tunani akan kusanci da juna da umarni guda biyu sukayi cikin Fadinsa madaukakin Sarki : [ Yaku Wadanda sukayi Imani Idan kun hadu da wata Jama’a – wato kafirai kenan a Yaki – To ku tabbatu, kuma ku ambaci Allah da yawa…] [Sur. Al-anfal- 45]. Ya sanya Zikiri a matsayin mafi girman abinda yake temakawa wajen tabbatuwa a fagen Jihadi.

“ Kuma kayi tunanin Rumawa da Farisawa a Yakukan da’akayi da kuma Masu Zikiri duk da Karancinsu.

Sannan da Menene Annabi Yusuf (Alaihis Salam) Ya samu Tabbatuwa sanda Fitinar Matannan me mulki da tsananin Kyawo ta nemeshi akanta? Shin be shiga cikin Ganuwan (Ma’azal lah) ba Ma’ana Ina neman kariya daga Allah kuma shin rundunar Sha’awa bata bal-balce ba akan katangan da suke kareshi?.

To hakane Yin Zikiri yake aiki wajen Tabbatar da Muminai.

HANYOYIN TABBATUWA NA UKU (3)

NA SHIDA: MUSULMI YAYI KWAɗAYIN BIN INGANTACCEN TAFARKI

Ingantaccen tafarki ƙwãya ɗaya tal, daya zama tilas kowani musulmi yabi, shine: tafarkin Ahlus-sunnah wal-jama’a. tafarkin Jama’a da’aka temaka, kuma Jama’a ne tseratattu, mãsu tsabtatattan Aƙida, da manhaji ingantacce, da bin Sunna da dalili, da banbanta daga maƙiyan Allah, da rabuwa da masu ɓata.

Idan kuma har kanã so kasan matsayin bin ingantaccen tafarki, a wajen tabbatuwa, to kayi tunani, kuma ka tambayi kanka: Me yasa dayawa daga cikin wadanda suka gabãta da wadanda suka biyo bãyansu suka halaka, kuma suka ruɗe, duga-dugansu suka kãsa tabbata akan tafarki madai-daici? kuma basu mutu akansa ba? Ko kuma A’A sun isa zuwa gareshi bayan sun ƙãrar da mafi yawan rayuwarsu, kuma sun ɓatar da mafi tsãdan lokutansu a cikin rayuwansu?.

Zakaga ɗayansu yana ta yãwo, a cikin masaukai na bidi’a da ɓata, daga Falsafa zuwa ga ilimin kalami wato zance, daga Mu’utazilanci zuwa ga Tahrifi da tãwili zuwa tafwidi zuwa ga Murji’anci, daga wata darik’a cikin Sũfanci zuwa wata.

To haka Y’an bidi’a, sũma sunã da rũɗu, da rashin natsuwa, ka duba kaga yanda aka hanãma Y’an Zance (wato Ahlul kalam) tabbatuwa a lokacin mutuwa, magabata Sukace: “Wanda sukafi kõwa Shakka a lokacin mutuwa sune Y’an Zance (Ahlul kalam)”.

Sedai kayi tunani kaga, shin akwai koda mutum ɗaya daga cikin Ahlus Sunna wal-jama’a, da yataɓa barin tafarkinsa, ya ƙyamaceshi, yayi fushi dashi, bayan yã bishi, yã sanshi, yã fahimceshi? Zata yiwuwa, Mutum ya barsa Saboda son rai, ko dan kwaɗayin abin duniya, ko saboda Shubuha da’aka bijiroma hankalinsa me rauni da’ita, Amma baya barinsa, saboda wai yaga wani tafarkin da yafishi inganci, ko yagãno cewa shi ɗin ɓatane.

Kuma abinda ze gaskata hakan shine: Lokacin da Hiraƙal ya tambayi Abũ Sufyan, gameda mãsu bin Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallamr, Se Hiraƙal Yace ma Abũ Sufyan: “Shin a cikinsu akwai koda Mutum ɗaya da yataɓa yin RIDDA -wato ya fita daga Addinin-, ya yi fushi dashi ya ƙyamace shi, bayan ya shiga cikinsa?” Se Abũ Sufyan Yace: A’a se Hiraƙal Yace: To hakanan Imãni yake, idan ya cakuɗa –wato ya haɗu- da Zũciya”.

Sau dayawa Munji cewa Shugabanni sun bar Masuaki na Bidi’a, wasu kuma Allah ya shiryasu, sun b’ar ɓata sun koma zuwa ga Mazhabin Ahlus Sunna Wal-jama’a, suna masu nuna ƙyama da fushi ga tafarkin da suke a kansa na farko,

Shin ko mun taɓa jin Akasin hakan?!

To idan har kanã son tabbatuwa, to wãjibi ne kabi tafarkin Muminai.

NA BAKWAI: TARBIYYA:

Tarbiyya ta Imãni da ilimi da fahimta, wanda take akan mataki - mataki, Ma’auni ne daga cikin ma’aunan Tabbatuwa.

TARBIYYAN IMANI: Itace take kãre zukãta da rãyuka. kuma Ana samun ta ne ta hanyar Jin tsoron Allah, da fãta, da Soyayya, wandu suke kõre bũshewar zuciya, sakamakon yin Nisa da Nassosin Alƙur’ani da Hadisan Manzan Allah Sallallahu Alihi Wasallamr, da durƙusãwa ga Zantuttukan Mazaje.

TARBIYYA TA ILIMI: Itace wacce take tsaye akan dalili ingantacce, wanda take kõre yin taƙalidanci da ….makoma…. abin zargi.

TARBIYYA TA FAHIMTA: Itace wacce da ita zãka san tafarkin mãsu laifi (mujurimai), da karanta Shirye-Shiryen maƙiya Musulunci, kasan abubuwan da suke fãruwa a gefenka, ka fahimci abubuwan dasuke fãruwa, dan ka iya yin hukunci akansu, Hakan ze kõre maka dõɗewa da zama a wuri ɗaya da rashin fita daga cikin bi’a da take Y’ar karama Iyakantacciya.

TARBIYYAN MATAKI-MATAKI: Itace Wacce zatabi da Musulmi da kaɗan da kaɗan (da sannu da sannu), har ta ɗagãshi zuwa ga matakin da ze cika, da tsari dai-daitacce, wanda hakan ze kõre masa Yin gaggawa da sauri da tsallake, wanda yake ruguzawa.

Kuma domin mu san mahimmancin wannan gaɓan cikin sassan tabbatuwa, to se mukoma zuwa ga Tarihin Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasllamr, kuma muyiwa kawunanmu tambaya?

**Menene asalin abinda ya tabbatar da Sahabban Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, a lokacin da’ake gãna masu Azãba?

** Me yasa Bilãl da Khabbab da Mus’ab da Ãlu Yãsir da sauransu, daga cikin masu rauni, kai har Manyan Sahabbai sũma a killacewan da’akayi musu a Bani Shi’ab da sauransu?.

** Shin zeyiwu tabbatuwansu ta kasance ba tãre da wata Tarbiyyaba me zurfi ba daga Fitilan Annabta, wanda ta tarbiyyantar da rãyukansu?

Mu ɗauka wannan Sahabin ƙhabbãb binil Art t Allah yakãra Yarda a gareshi, wanda Shugabansa ta kasance tana ƙõna wayã, irin wanda ake gasa nãma dashi, har se tayi Jãjur, sannan se ta ɗõra bayansa akai –wato tana gasa bayansa kaman nãma kenan a bũɗe –, Kuma Mai dake fitõwa daga bayansa ne, idan ya kwararo, yake kasheta. To Me yasa yayi haƙuri akan haka?

Bilãl Kuma yana cãn ƙarƙashin dũtse a kan Sahãra, SUMAIYA kuma tana ɗaure cikin Mari. Gawata tambaya da’aka samu a Lokacin dasuke Madina: Su wãnene suka tabbata tãre da Manzan Allah Sallallanu Alaihi Wasallam r a Yaƙin Hunãin lõkacin da aka sãmu Nasara akan dayawa daga cikin Musulmai? Shin Sãbabbun Musulunta ne, ko wanda suka musulunta a Yãƙin Makka, wanda basu sami isasshen lõkaci na tarbiyya ba a Makarantar Annabta, wanda dayawa daga cikinsu sun fita ne saboda neman Ganima? A’a...Mafi yawa cikin waɗanda suka tabbata sune: waɗannan zãɓaɓɓun Muminan, da suka sãmu adadi me girma na Tarbiyya daga wajen Manzan Allah Sallallanu Alaihi Wasallam r . Ba domin akwai Tarbiyya ba, Shin kãna ganin waɗannan Sahabban zãsu tabbata?

TAMBAYA : Hadisin dayake cewa “ Kada kuyi Azumi ranar Asabar Face abinda aka Farlanta maku – wato Ramadan –“ shin Hadisin Ingantacce ne, kuma menene ma’anar Hadisin kuma shin ya kunshi dukkan Azumi ne?

ME BADA AMSA: Shaikh Abdur rahman bin Jibrin Mamba a cikin Majalisar manyan malamai masu fatawa a kasar Saudi Arabia.

AMSA: an kebance ranar Asabar ne da Hani saboda yahudawa sun kasance suna barin aiki a cikinta, se aka hana girmama ranar saboda kada ayi kamance – ceniya dasu, kuma ya halarta a Azumce Asabar idan akwai sababi, Kaman wanda yake Azumi rana ya sha ruwa rana, haka idan yayi dai- dai da ranar Arafa, ko Ranar Ashura da makamantansu, Ma’anar (abinda aka Farlanta maku) ma’anarsa aka shar’anta, kuma aka sunnanta maku.

23 Mar 2008

SHIN KE MACE CE ME KAMA DA MAZA WAJEN KOKARI?! GA WASU HANYOYI GUDA GOMA ‎DOMIN KIZAMA HAKAN

Abune dayake sananne cewa kina fuskantar matsaloli cikin ranki da kuma zamantakewa a wajen kulla Alaka da aikace - aikacenki, to abinda yakamata kisani shine rayuwa bata rabuwa da wadannan matsalolin, kuma babu shakka nasan cewa sau dayawa kin yi tunani akan wata matsala da ta faru dake, bayan kin dauka mataki domin kiga shin kinyi dai dai koko shin kin yi kuskure? akan matakin dakika dauka, daganan kina kara samun kwarewa wajen magance matsalolinki, ba’a baukatan koda yaushe kizama me ran karfe wajen war - ware matsaloli, amma ga wasu abubuwa dazasu temaka maki wajen hakan

  1. Kiyi abinda ake kira jeranta abubuwa gwargwadon muhimmancin su wato (First thing First) kuma ki tsara ayyukanki,, hakan ze kareki daga damuwa, saboda kina zartar da abinda yakeda muhimmanci sosai, kuma ze rage maki damuwa, saboda ayyukan da bakiyi su ba, basu da muhimmanci sosai.
  2. Kada ki dora ma kanki abinda yafi karfinki, Allah Madaukakin Sarki yace: (La yukallifullahu nafsan illa wus aha Suratul Bakara 286. Ma'ana Allah baya kallafa ma rai face abinda take iyawa. To ya tausaya mana saboda haka yakamata mu tausaya ma kawunanmu, amma batare da kasala ba ko rashin yin aiki, kuma kada kice se kinyi komai da kikeso, wato ki cika komai, domin cika na Allah ne kadai, takenki yazama “Adai daita sahu”
  3. Kada ki shagaltu da aiki fiye da daya, a lokaci guda domin ze kasa hankalinki biyu da kokarin dakikeyi, daga nan baza ki iya yin aiki kwakkwara ba me aminci, abinda yakamata shine: ki kammala wani sannan ki fara nagaba dashi, domin hakan ze saki jin dadi da jin cewa kina samun nasara a rayuwa, kuma ze sa kiyi kwadayin aiwatar da wani aikin.
  4. Wajen alakar ki da sauran jama’a kuma: kiyi kokari ki fuskance su da rashin yin karya kuma bada barin gaskiya ba, A’a cikin natsuwa da hankali, kuma kada kiyi fushi, idan wasu basuyi kawance dake ba, haka kuma ki karbi kuskure idan anyi maki gyara, sawa’un daga kawayenki ne ko wasu daban, ki dauki hakan a matsayin jarrabawa na fadada kirjin ki (wato koyan yin hakuri).
  5. kada kibar jarabawa da baki samu nasara ba akanta, ta hana ki aiwatar da wani aiki, yin tunani akan abinda baki samu nasara ba akansa zesa kiyi wanda yafishi kyau, abinda ya kamata ki dauki rashin samun nasaranki a matsayin ma’auni na samun darasi da kwarewa. Ba matsayin tsoro ba.
  6. Wajen alakanki da sauran jama’a, ki dinga kokarin yawan mur mushi, kuma ki tuna da hadisin da ke cewa “ Yin mur mushin ka ga dan uwanka SADAKA ne" – (wato akwai lada a cikinsa) kuma ki sani dariya na kara maki soyayya dake sa zuciya ta natsu, kuma kiyi kokarin yin Magana da sauti dan kadan domin daga sauti na kara rashin jituwa.
  7. Likitoci suna cewa: Cakuda jiki yana temakawa wajen rage rashin natsuwa da damuwa, To saboda haka ki kwatanta kigani, musamman wajen wanka, da lokacin alwala ki dinga caccakuda yatsun hannu da na kafa.
  8. Ki yi kokari ki dinga yin Zikirin Safiya da na Marece, ze saki a koda yaushe kizama kina tareda Allah, kuma ze kara maki jin cewa Allah yana ganinki a koda yaushe, kuma kina cikin Kariyarsa, kuma kina da ikon ketare kowani abu dayake da wahala, da war - ware matsaloli da datarwansa (ikonsa), ki rokeshi dacewa, da yin dai - dai, Shi Allah yana yaye bakin ciki, kuma yana amsan rokon wanda ya kirasa (mabukaci).
  9. Kada ayyuka ko damuwa susa ki dinga jinkirta sallah, SALLAH hutu ce ga rai kuma natsuwa ce ga zuciya, Kuma Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya kasance yana cewa “Bilal ka hutar damu da Sallah” lokacin da zece ya tada ikama.
  10. Kada kiyi kokarin Boye rashin jin dadinki da damuwanki, A’a kiyarda cewa kinada damuwa, amma ki amince cewa kina da ikon da zakiyi nasara akansa, kuma idan kikaji cewa kinaso kiyi kuka, to kada kiyi kokwanto kiyi kuka da hawaye domin yin kuka ba dalili ne na rashin iko ba ko shi ke nuna kina da rauni, a’a kuka hanya ne na rage damuwa da rai ke ciki.

20 Mar 2008

HUKUNCIN SHAN TABA DA WIWI

Shan Taba ko Wiwi da makamantansu abubuwane da Addinin Musulunci ya haramta ga dalilai akan haka :- Fadin Allah Madaukakin Sarki : ( Kada ku kashe kawunanku, Lallai Allah mai jinkai ne akanku ) da Fadinsa : ( kuma kada ku jefa hannayenku zuwaga hallaka) wato kada kuyi duk abinda zezama sanadiyyar hallakanaku, kuma likitoci sun tabbatar da cewa Shan taba da Wiwi suna cutarwa, saboda haka abinda yake cutarwa haramun ne. ga wani dalilin kuma Allah Madaukakin Sarki Yace: ( kuma kada kuba wawaye dukiyoyinku wanda Allah yabaku) Ya hana muba wawaye kudadenmu saboda suna lalatardasu da bannatawa, kuma babu shakka sayen taba da wiwi barnan kudine, kuma yana cutar da mai sha d a kuma wanda yake shakan hayakin, kuma ance wanda yake shaka yafi cutuwa akan me shan, kaga kenan laifi biyu ne, na farko cutar da kai da ayoyin baya suka hana, na biyu cutar da waninka da shima Addini ya hana. Saboda haka aka haramta shan taba da wiwi da dalilin hanin wancan ayan da kuma Fadin Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya hana wulakanta kudi, Yace: ( babu cuta kuma babu cutarwa) kuma shan wadannan abubuwa na samarda cutarwa, kuma in mutum yasaba dasu, yanada wahala ya iya barinsu , idan be same suba yana samun kunci cikin ransa, kai duniya matayi mai kunci, kaga ko wannan ya isheshi fitina. Allah ya karemu.

13 Feb 2008

NA FARKO: FUSKANTAR ALQUR’ANI: .

HANYOYIN TABBATUWA AKAN ADDININ ALLAH, Maudu’ine me muhimmanci saboda:* Halin da Musulmai suke rayuwa a ciki a Yau, da Nau’I daban- daban na fitintinu da abubuwan rud’i da dangogin ababen Sha’awa da Shubuhohisaboda yanda zamani ya lalace, da karancin na kwarai, da raunin matemaki da karancin masu temakawa, Yin ridda da komawa kafirci da juyewa yayi yawa,Hanyoyin tabbatuwa domin ya kaiga tsira. wanda ta dalilinsu ne musulunci ya wayi gari yana bak’o , se wadanda sukayi riko dashi suka zama kamar yanda karin magana ke cewa: “Wanda yake riko da Addininsa kamar wanda ke riko ne da garwashin wuta”. .

9 Feb 2008

HANYOYIN TABBATUWA AKAN ADDININ ALLAH NA (2)

NA BIYU: BIN DOKOKIN ALLAH DA AYYUKA NA KWARAI:

Allah Madaukakin Sarki Yace: [Allah yana tabbatar da wadanda sukayi Imani da zance tabbatacce a rayuwar duniya da kuma a lahiha kuma Allah yana batar da Azzalumai kuma Allah yana aikata abinda yaga dama] [Sur.Ibrahim -27]. Imamu Qadata Yace: “Abin nufi da a rayuwar duniya shine: ya tabbatar dasu akan alkhairi da aiki na kwarai, kuma abin nufi da: a lahira wato a cikin kabari”, kuma an ruwaito hakan daga fiye da mutum daya, daga cikin magabta [Tafsirin Ibn Kathir Vol.4 p.421.] Kuma Madukakin sarki Yace: [Da’ace sun aikata abinda akeyi masu wa’azi, da hakan yazama alkhairi agaresu, kuma da yafi k'arfi wajen tabbatarwa] [Sur. Nisa’i-66]. wato akan gaskiya. Kuma wannan a bayyane yake, in ba haka ba, Shin muna tsammanin samun tabbatuwa daga wajen masu kasala, wadanda basa aikata ayyuka na kwarai a lokacin da fitina zata turo kanta, kuma huduba zata……..? Amma wadanda sukayi Imani kuma sukayi aiki na kwarai Ubangiljinsu ze shiryar dasu zuwaga tafarki na kwarai saboda Imaninsu, domin haka ne Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya kasance yana yin Umarni da dauwama akan ayyuka na kwarai, kuma aikin da yafiso shine wanda aka dauwama akansa koda ko dan kadas n ne, kuma haqka Sahabbansa sun kasance idan sukayi wasni aiki to suna tabbata akansa.

Nana A’isha Allah yakara Yarda agareta, ta kasance, idan ta aikata, wani aiki tana lazimtarsa. Kuma Ma’aiki Sallallahu Alaihi Wasallam Ya kasance Yana cewa: “Duk Wanda ya dauwama akan yin Raka’a goma sha biyu to Aljanna ta tabbata agareshi” [Tirmidhi Vol.2 No. 273 Nasa’I Vol.1 No. 388]. (Abin Nufi: Nafiloli da'akeyi kafin salloli na farilla da bayansu), kuma yazo cikin Hadisi Qudusi: “kuma bawa baze gusheba yana kusantuwa zuwa gareni, da aikata Nafiloli har in so shi” Bukhari.

NA UKU: TADABBURIN (YIN TUNANI AKAN) K’ISSOSHIN ANNABAWA DA BINCIKE AKAN HAKAN DOMIN YIN KOYI DA AIKI: Kuma dalili akan haka Fadansa Madaukakin Sarki: [ Kuma kowanne daga cikinsu muna baka K’issarsa, daga labarin Manzanni gwargwadon abinda zamu tabbatar da zuciyarka dashi, kuma akan hakan Gaskiya tazo maka da wa’azi da tunatarwa ga Muminai] [Sur. Hud – 120]. Kuma wadannan Ayoyi ba'a saukar dasuba, a Zamanin Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam domin wasa ko ba’a, A’a an saukar dashi ne, domin wata Manufa me girma, itace: Tabbatarwa ga zuciyar Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasllam da kuma zukatan Muminai dasuke tare dashi.

To D’an Uwa! idan kayi tunani gameda faɗin Allah Madaukakin Sarki: [Sukace: ku k’onashi kuceci gumakanku, idan kun kasance masu aikatawa, se mukace: Yake wuta kizama me sanyi da Aminci ga Ibrahim* se sukayi nufin makirci akanshi se muka sanyasu sune masu Asara] [Sur. Al-Anbiya’i : 68-70] . Abdullahi dan Abbas Allah yakara masa yarda Yace: “Maganar k’arshe da Annabi Ibrahim Yayi da’aka jefashi cikin wuta shine: (Hasbiyal lahu Wani’imal Wakil)”. Ma’ana Allah ya’isar mun kuma madalla da abin dogaro. Shin bakaji wata ma’ana ba, daga ma’anonin tabbatuwa ta shiga cikin ranka – a gaban masu dagawa da Azaba – lokacin da kake karanta wannan K’issa?

Idan kayi tadabburin (tunani akan) Faɗen Allah Madaukakin Sarki a cikin K’issar Annabi Musa: [A lokacin da sukaga tarun runduna, se mutanen Musa sukace: tabbas zasu riskemu * Yace: A’a Lallai ina tareda Ubangiji na, ze shiryar dani] [Sur. Ash Shu’ara’I: 61-62] . Shin bakaji wata ma’ana ba, daga ma’anonin tabbatuwa lokacin haduwa da Azzalumai, dajin tabbatuwa a lokacin tsanani, sanda masu yanke tsammani suketa ihu, a lokacin da kake karanta wannan k’issar?. Haka da zaka bijiro da K’issar mutanen Fir’auna masu Sihiri, Wannan Asali ne me ban sha’awa, na jama’an da suka tabbata akan gaskiya, bayan bayyananta agaresu. Shin bakaga ma’ana me girma daga ma’anonin tabbatuwa wanda yake zama a cikin zuciya a lokacin da Azzalumi yake bada tsoro -wato Fir'auna kenan- Yana cewa: [ Yace: Yanzu zakuyi Imani dashi, tun kafin inyi muku izini, lallai shine babbanku wanda ya karantar daku Sihiri, To Wallahi zan daddatse Hannayenku da kafafuwanku daban daban, kuma Wallahi zan tsireku a kututturen dabino, kuma Wallahi zaku san wanene cikinmu yafi tsananin Azaba kuma tafi wanzuwa ] [Sur. Taha: 71]. Tabbatuwan Muminai Y’an kaɗan, wanda ko kad’an suka ƙi su dawo kan ɓata, kuma suka ce: [ har abada bazamu fifitaka ba akan abinda yazo mana daga Ubangijinmu na gaskiya, kuma shine wanda ya k’agi halittanmu, ka zartar da abinda zaka aikata, kawai zaka zartar da abune a wannan rayuwan ta duniya] [Sur. Taha: 72]. Hakanan K’issar Muminin nan a cikin Suratu Yasin da Muminin Suratu Ali’imrana da Ashabul Ukhdud wato Ma’abota raami da sauransu kusan tabbatuwa kusan shine babban darasin dake cikin dukkansu.

NA HUDU: YIN ADDUA: Yin Addu’a yana daga cikin Siffofin Bayin Allah Muminai shine suna fuskantar Allah, da Addu’a daya Tabbar dasu, suna cewa: ** Ya Ubangijinmu kada ka karkatar da zukatanmu bayan ka shiryar damu. (Rabbana La tuzig ƙulubana ba'ada iz hadaitana) ** Ya Ubangijinmu ka bamu wani irin Hakuri kuma ka tabbatar da diga –digan mu. (Rabbana afrig alaina Sabran) Kuma tunda “ Dukkan Zukatan Y’an Adam suna tsakanin yatsu biyu ne daga yatsukan Ubangiji kamar zuciya ce k’waya d’aya yana juyasu yanda yakeso” Imamu Muslim da Ahmad . Shiyasa Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, yake yawan faɗin: “Ya me jujjuya zukatu ka tabbatar da zuciya ta akan Addininka” Tirmidhi

17 Jan 2008

ASHURA…… BIKIN SAMUN NASARA AKAN MASU DAGAWA.

ASHURA…… BIKIN SAMUN NASARA AKAN MASU DAGAWA.

Goma ga watan Muharram (Ashura ranace da Allah ya Girmama, kuma Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yayi bikinsa kuma yayi Umarni da Azumtansa, kuma yace gameda Ashura: Ashura wata ranace daga cikin ranakun Allah Madaukakin sarki, kuma wannan rana an kasance ana girmamata a lokacin jahiliyya, kuma yahudawa sun kasance suna daukansa a matsayin Idi, kuma shine Azumi na farko da’aka farlanta akan Musulmi kafin Ramadan.

Imamul Bukhari da Muslim sun ruwaito daga Abdullahi dan Abbas Allah ya k’ara yarda agaresu Yace:- “Yayinda Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasalllam Yazo Madina, ya sama yahudawa suna Azumtan Ranar Ashura, se Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Yace: “Ku bani labarin wannan rana da kuke Azumta, se Sukace: “wannan ran ace me girma Allah ya tseratar da Musa da Mutanensa a cikinta, kuma a cikinta y a halakar da Fir’auna da mutanensa se Annabi Musa yayi Azuminsa , a matsayin godiya ga Allah, saboda haka muma muke Azuminsa, se Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Yace: “To mu mukafi dacewa da Can- Canta da Musa akanku , se Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasllam Ya Azumcesa kuma yayi Umarni da’ayi Azuminsa”

Kuma gameda Falalar Azumin wannan rana Yazo a cikin Hadisi me tsawo cikin Sahihu Muslim daga Abu Qatada Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Yace:- “ kuma Azumin ranar Ashura Ina fatan Allah ya kankare zunuban shekara da ta gabata dashi”

kuma yazo cikin Sahihul Bukhari daga Abdullahi dan Abbas Allah Yakara masa yarda Yace: “Banga MAnzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya kebance wata rana da Azumi kuma yana Fifita Azuminsa akan waninsa ba se Azumin ranar Ashura , da wannan watan wato watan Ramadan.

Kuma sirrin dake cikin Azumin wannan rana shine: Nasara da Allah yabawa Annabi Musa da Mabiynsa da Halakar da Fir’auna da rundunarsa, wato biki ne Goyon baya da Allah yaba Muminai wanda sukayi Annabinsu biyayya kuma suka fita tareda shi domin su kafa wata kasa ta Musulunci sabuwa, kuma farin ciki ne da karya zalunci da dagawa dake tare da Fir’auna da rundunarsa wadandz suka yi dagawa a cikin garin Misra kuma suka yawaita barna a cikinisa.

Kuma Sirrin dake cikin rashin Can- Cantan Yahudawa da yin Bikinsa, da yin bikin Samun Nasara akan dagawa shine: Yahudawa sun shika cikin Ayarin masu Dagawa da Zalunci da girman kai, kai a yanzu ma sun zama sune Jagorin sa a duniya, saboda haka basu daceba da yin bikin wannan tunawan me girma. Saboda mu mukafi Can- Canta da Annabi Musa akansu, Mune masu yin Bikin, kuma muke da bam-bamci a bikin da yin Azumin Ran ta Goma da ta Tara ko ta Sha d’aya saboda mu sab’ama Yahudawa masu dagawa kamar yada Manzan Allah Salllallahu Alaihi Wasallam ya Umarcemu dashi.
BIKIN BAK’IN CIKI (TA'AZIYYA) NA Y’AN SHI’A RANAR ASHURA

Wannan hoton yanda Shi'a suke kunna kyandura kenan a daren Ashura irin Yanda kiristoci sukeyi.

BIKIN BAK’IN CIKI NA Y’AN SHI’A (TA'AZIYYA)

Amma gameda Ta’aziyyan Shi’a, babu wanda yake jayayya akan Falalan Husaini Allah Yakara yarda agareshi , da Darajojinsa domin ai yana daga cikin Malaman Sahabbai, kuma shugaba ne na Musulmai a duniya da Lahira wadanda aka sansu da Bauta da Jarumtaka da Yalwa… kuma shi d’ane wajen Y’ar mafificin halittu Sallallahu Alaihi Wasallam, itace mafificiya a cikin Y’ayansa, kuma abinda yafaru na kisansa Al’amarine abin k’i mummuna me bak’anta rai a wajen kowani Musulmi, kuma hakika Allah ya dauki fansa daga wanda suka kasheshi, Inda ya wulakantasu a duniya kuma ya sanya su suzama wa’azi, bala’o’I da fitinu suka samesu kuma kad’an ne suka tsira daga cikinsu, kuma me yasa bama ganin shugabanninsu suna zuwa suna Yanka jikinsu kamar yanda sauran mutane keyi ?

Kuma abinda ya kamata a lokacin tunawa da musiban kashe Husaini da makamancinta shine: Hakuri da Yarda da hukuncin Allah da k’addararsa kuma shi Allah yana zab’awa bawansa abinda yafi zama Alkhairi, Sannan Neman Lada wajen Allah madaukakin Sarki sakamakon Hakurin.

Amma be da Kyau ko kad’an abinda muke gani Shi’a na aikatawa na bayyana b’akin ciki da rashin hakuri wanda suka kirkiro kuma suka kallafa ma kansu, Mahaifinsa Aliyyu wanda yafishi Falala shima an kashe shi to meyasa basu rik’I mutuwarsa amatsayin abin ta’aziyya ba? kuma an kashe Usmanu da Umar kuma Abubakar yarasu Allah yakara masu yarda kuma dukkansu sun fishi falala… kuma shugaban Halittu Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam ya rasu kuma ran mutuwansa ba’ayi abinda yake faruwa ba a ranar Kisan Hussaini, kuma yin bikin Bak’in ciki? Baya cikin Addini kai yafi kama da ayyukan Jahiliyya ( Alfatawa : Vol. 25 p. 307-314, da Iqtida’us siratal mustaqim Vol. 2 p.129 – 131.)

Imamu bin Rajab Yace gameda Ashura: Amma rik’onsa a matsayin Biki na Bak’in ciki, kamar yanda Rafidawa sukeyi, saboda kisan husaini Allah yakara yarda agaresu, yana daga cikin ayyukan wanda ya bata ayyukansa a duniya alhali yana tsammanin ya aikata aiki maia kyau, kuma Allah da Manzansa basuyi Umarni da rik’o da ranakun da Annabawa suka fuskanci Musiba da Ranakun Mutuwansu a matsayin Biki na Bak’in ciki, to yaya za’ayiwa wanda be kaisu ba, (Lata’iful Ma’arif P.113) kuma abin lura shine Matim na Rafidawqa a ranar Ashura baya da Alak’a da Musulunci a kusa ko a nesa, domin baya da alaka da Tseratar da Annabi Musa ko da Azumin Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, kai a fili yake ma sun musanya wannan Munasabar zuwa ga wani abu na daban, kuma wannan yan daga cikin Asalin Musanya Addinin Allah Madaukakin Sarki
Yaro kenan yake sarar kansa da Wuka ranar Ashura
Nan Suna dukan jikunansu ne da bulalan dalma
Dan K'aramin Yaro ma be tsira ba daga ta'addancin Bikin Bakin ciki na Y'an Shi'ah

Wannan Hoto na Yan Shi'ah Kenan Yanda suke yanka jikunansu a Ranar Ashura Shin wani irin Addini ne wannan?
Domin kagane ma idanunka hakan kana iya kallon talabijin ranar Ashura kaga yanda Y'an Shi'a a kasar Irak'i suke aikata wannan aikin saboda Akida dasuke da ita cewa dolene kowa yazubar da jininsa kamar yanda aka zubar da jinin Husaini Radiyallahu Anhu a wannan rana. To amma me yasa Mlumansu basa aikata hakan se akabar talakawa? Allah ya kiyayemu Amin

AYYUKAN MUTANE RANAR ASHURA A MA’AUNIN SHARI’AH

Wanda ke lura da al’amura ayau ze ga cewa suna kebance ranar Ashura da abubuwa masu yawa:- daga ciki akwai:-

* Azumi munyi bayanin matsayinsa a cikin Shari’ah,

* Akwai raya daren Ashura, da kwad'ayin kuntatama kai wajen yin abinci da yanka iri daban- daban na nama, da bayyanar da Murna da farin ciki.

* Akwai abubuwa dake faruwa a garuruwa daban- daban na ta’aziyya, da bak'in ciki ta hanyar aiwatar da wasu abubuwa na daban kamar yanda Rafidawa (Shia’a) sukeyi da wasunsu.

Yakamata musan matsayin wadannan ayyukan a shari'a, daganan suna iya zama ayyukan neman lada da kusanci zuwa ga Allah, ko kuma sanin rashin shar’antasu, se suzama bidi’ah da zasu nesanta mutum ga Allah.

To dolene mu sani cewa: ayyuka a wajen Allah basa samun karbuwa se sun cika wasu sharudda daga ciki akwai: Me yin aiki ya kasance yana me koyi da Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, to idan muka duba ayyukan mutane a ranar Ashura sawa’un abubuwanda sukeyi a baya ko a wannan lokaci zamuga cewa suna da Nau’o’I daban daban:

1. akawai abinda yake na bauta : sun ware wwannan rana das wasu bauta na dabam kamar yin tsayuwa cikin daren Ashura, da ziyartan makabartu a cikinsa, da yin sadaka, da bada zakka, da karanta surorin da akwai ambaton Annabi Musa a cikinsu a alfijirin ranar Ashura… wannan da wasunsu, ayi abinda yasaba acikinsu wato dalilin yin aikin shine kebance shi da wani lokaci da Allah be ce a kebance su dayin hakan ba, kuma idan da Allah naso a aikata hakan to da yayi umarni da kwadaitar da yin hakan, kamar yanda ya kwaidaitar da yin Azumi a cikinsa.

To kenan an hana kebance wani lakaci da yin wata ibada ta daban, koda kuwa ace aikin shi karan kansa akwaishi a shar’aih wato ba'a haramtashi ba.

2. abinda yake Al’ada ce ake aikatawa, a ranar Ashura, irin wanda akeyi a Idi daga cikinsu akwai:-

* Yin wanka da sa kwalli da sanya turare da yalwata ma Iyalai a abinci da abin Sha da dafe dafe da toye- toye da yin yanka da bayyana Murna da farin ciki.

* kuma akwai wasu al’adu da suke cike da abin muni, kuma dukkan wadanna abubuwa sun samo asali ne a matsayin mayar da martani ga ta’aziyyan Rafidawa dasuke yi na nuna bakin ciki ga Mutuwan Husaini Allah yakara yarda agareshi, (To se Nasibawa sune wadanda suke nuna k’iyayya ga Ahlul baiti suke kishiyantan Shi’a wato rafidawa, wadanda su kuma suka wuce Iyaka wajen Ahlul baiti) da bayyana zagi garesu da nuna farin ciki, suka kirkiro abubuwan da babu su cikin Addini se suka fad’a cikin kamanceceniya da Yahudawa wajen daukansa a matsayin Idi wato biki kamar yanda ya gabata. (Kamar yanda Shaikhul Islam ya ambata a cikin littafinsa Iqtida’us siratal mustaqim Vol-2 p. 129-134).

* Yin Wanka kuma da sanya kwalli…..babu wani abu acikinsu da ya tabbata.

Imamu Bin Taimiyya yayi nuni ga Hadisan da sukazo dake nuna falalan Ashura yake cewa: dukkaninsu k’arya ce da’akayi wa Manzan Allah, babu wani abu daya inganta a cikinsa in banda Azumi, kuma wannan shine tafarkin Manzan Allah Sallalllahu Alaihi Wasallam.

Allah Madaukakin Sarki yace: "Hakika koyi me kyau ya kasance agareku daga Manzan Allah, ga wanda yake fatan Allah da Rana ta K’arshe kuma ya( ambaci Allah da yawa” Sur. Al-Ahzab -12.

kuma dayawa daga cikin wadannan da suke shagaltuwa da bidi’o’I, dayawa bin ManzanAllah Sallallahu Alaihi Wasallam na wuce su da bin aiki da Sunnarsa.