MARABA DA ZUWA SHAFINMU NA MUSULUNCI

2 Jan 2008

TARE DA MANZAN ALLAH SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM NA (2)

SUNA DA DANGANTAKAN MANZAN ALLAH SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM

1. Allah Madaukakin Sarki Yace:- ( Muhammadu Manzan Allah ne ..)Sur. Fathi -29.

2. Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasllam Yace: ( Ina da Sunaye guda biyar : Nine Muhammad , kuma Nine Ahmad, kuma Nine Maahi -wato ma’ana me shafewa -, wanda Allah yake shafe kafirci dani, kuma Nine Alhashir -wato ma’ana me tara jama’a.-, wandaza’a tara mun mutane a gaba na, kuma Nine Al’aqib-wato ma’ana na K’arshe.-, wanda a bayansa babu wani Annabi) Bukhari da Muslim.

* Kuma Allah Yayi masa suna da Ra’uf -wato ma’ana me matuk’ar tausayi- da Rahim -wato ma’ana me Jinkai-

3. Kuma Manzan Allah Yakasance yana ambata mana Sunayensa se yace: ( “Nine Muhammad Nine Ahmad, Nine Almuqaffa, Nine Alhashir. Kuma Nine Annabin Tuba, kuma Nine Annabin Rahama”). Muslim

4. Kuma Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasllam Yace: ( “ Shin be isheku ba yazama abin Mamaki, yanda Allah yake kawar mun da zagin K’uraishawa da La’antansu? Suna zagina da Muzammam, kuma suna la’anta na da muzammam, Alhali kuwa Ni Muhammad ne”) Bukhari.

Ma’noni: Muzammam abin zargi.

5. Kuma Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasllam Yace: ( “ Lallai Allah Yazabi Kinana daga Y’ay’an Annabi Isma’il, Kuma yazab’i K’uraishawa daga Y’ay’an Kinana, kuma yazab’i Banu Hashim daga K’uraishawa, kuma yazab’eni daga Banu Hashim”). Imam Muslim

6. Kuma Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasllam Yace: ( “Kusnaya Sunayena, amma kada ku sanya Alkunyata, domin ni meyin rabo ne a tsakaninku”). Muslim.