MARABA DA ZUWA SHAFINMU NA MUSULUNCI

13 Jan 2008

HANYOYIN TABBATUWA AKAN ADDININ ALLAH (1) Bismillahir Rahmanir Rahim

Dukkan Yabo da Godiya sun tabbata ga Allah, Muna gode masa, muna Neman temako agaresa, kuma muna Neman Gafararsa, kuma muna Neman tsarin Allah da yakare mu daga sharrun kawananmu da Munanan ayyukanmu, Duk wanda Allah ya shiryar , to babu me batar dashi kuma duk wanda Allah ya batar to babu me shiiryar dashi, kuma Ina shaidawa Babu abinda ya Can-Canci bauta se Allah shi kadai baya da Abokihjn tarayya , kuma Ina Shaidawa Lallai Annabi Muhammadu Bawansa ne kuma Manzansa.

Bayan Haka: Tabbatuwa akan Addinin Allah abune da’ake nema wajen kowani musulmi na gaske da yake neman Tafarki Madaidaici tare da Himma da Shiriya.

Kuma wannan Maudu’in yanada muhimmancin saboda:

* Halin da Musulmi suke rayuwa a ciki a Yau da Nau’I daban- daban na fitintinu da abubuwan rud’i wanda da wutanta suke neman magani, da kuma dangogin Abubuwan Sha’awa da Shubuhohi wanda ta dalilinsu ne musulunci ya wayi gari yana bak’o , se wadanda sukayi riko dashi suka zama kamar yanda karin magana ke cewa: “Wanda yake riko da Addininsa kamar wanda ke riko ne da garwashin wuta”.

To babu shakka, duk me Hankali zega, cewa bukatan Musulmi a Yau, zuwaga Hanyoyin tabbatuwa tafi bukatan da dan Uwansa yake da’ita a lokacin Magabata, kuma kokarin daza’ayi wajen samun hakan shi yafi girma saboda yanda zamani ya lalace, da karancin na kwarai, da raunin matemaki da karancin masu temakawa.

* Yin ridda da komawa kafirci da juyewa yayi yawa, har hakan yasa wasu da sukewa Addini aiki suke jima musulmi tsoro ga makomansa kuma suke nema masa Hanyoyin tabbatuwa domin ya kaiga tsira.

* Batun yana daure da zuciya wanda Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Yace: “Wallahi zuciyar dan Adam tafi juyewa da tukunya idan ta tafasa” Ahmad da Hakim.

Kuma Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya buga wani misalin gameda zuciya Yace: “An sanyawa zuciya suna ne saboda juyawanta, lallai misalin zuciya kamar misalin ………ganye ko iri…. A Bishiya iska na kad'a cikinsa da wajansa” Ahmad.

To tabbatatar da wannan abinda yake jujjuyawa da guguwan Sha’awowi da Shubuhohi al’amarine da yake da hatsari , yana bukatan Hanyoyi masu karfi dazasuyi dai-dai da girman aikin da wahalarsa.

HANYOYIN TABBATUWA

Yana daga cikin Falalar Allah akanmu, da ya bayyana mana hanyoyi masu yawa na tabbatuwa akan Addininsa , a cikin littafinsa da kuma ta harshen Manzansa da Tarihin rayuwarsa, Sallallahu Alaihi wasallam.

Me Karatu zan bijiro maka da wasu daga cikinsu Kamar Haka:-

NA FARKO: FUSKANTAR ALQUR’ANI:

Alqur’ani me girma shine hanya ta farko na tabbatuwa, shine Igiyar Allah me karfi , shine Haske mabayyani , duk wanda yayi riko dashi Allah ze kareshi , wanda duk ya bishi to Allah ze tseratar dashi, kuma duk wanda yayi kira zuwa gareshi, za’a shiryar dashi zuwa tafarki madaidaici.

Allah madaukakin Sarki ya bayyana kololuwan manufar da tasa ya saukar da Alqur’ani a rarrabe, itace Tabbatuwa, Allah Madaukakin Sarki yace wajen mayar da martani ga Shubuhan kafirai: ( Kuma wadanda suka Kafirce suke cewa Inama da ace an saukar masa da Alqur’ani jimla guda ? Munyi hakan ne domin mu tabbatar dashi a zuciyarka, kuma mun jeranta karantashi da hankali jerantawa * kuma bazasu zo maka da wani misali ba , Face mun zo maka da gaskiya da kuma mafi kyawun fassara) Sur. Furqaan: 32-33.

Me Yasa Alqur’ani yazama Masdar wato tushen Tabbatuwa?

** Domin ya shuka Imani kuma ya tsarkake rai ta hanyar sadar da’ita da Allah.

**Domin wannan Ayoyin suna saukar da Sanyi da Aminci akan zuciyan Mumini, Guguwar fitina bazata share shi ba, kuma zuciyarsa zata natsu da ambaton Allah.

**Domin yana kara wa Musulmi tunani da Halaye na kwarai wanda dasu ne ze iya yima abinda ke kewayensa hukunci, to haka kuma ze bashi Ma’auni daze temaka masa wajen yima al’amura hukunci kuma hukuncinsa bazeyi rawaba, kuma zantukansa bazasu dinga war-ware juna ba saboda sabanin abubuwan dake faruwa ko mutane.

**Saboda yana mayar da martani ga Shubuhohi (wato abubuwa masu kama da gaskiya) da makiya musulunci suke samardasu daga wajen kafurai da Munafukai, kamar Misali me rai da Yan zamanin farko suka rayu dashi, wannan sune Misalan:

-Menene tasirin Fadin Allah Madaukakin Sarki: (Ubangijinka beyi ban kwana da kai ba kuma be kauracema ba -wato be k'ika ba-) Sur. Duha-3.

a cikin ran Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam lokacin da Kuraishawa sukace: “Anyiwa Manzan Allah ban kwana….”?

-Menene tasirin Fadin Allah Madaukakin Sarki: ( Harshen dasuke karkata zance dashi ba Ajame ne , kuma wannan Harshe ne na balarabe Mabyyani) Sur. Nahl-103. lokacin da Kuraishawa sukayi Ikirarin cewa wani mutum ne yake karantar da Annabi Sallallahu Alihi Wasallam Alkur’ani, kuma yana koyon Alkur’ani ne daga wajen wani kafinta ba rume a Makkah?

-Menene tasirin Fadin Allah Madaukakin Sarki: ( Ku saurara! A ciki fitiana suka fad'o) Sur. Tauba -49. a cikin zukatan Muminai lokacin da Munafukai sukace: Kayi man……”?.

Shin ba tabbatarwa bane akan tabbatarwa, kuma da daure zukatan Muminai, da kuam mayar da martani ga Shubuhohi, da kuma shiruntar da Masu bata?... ina rantsuwa da Ubangiji na Hakane.

Kuma yana daga abun mamaki, cewa Allah yayi wa Muminai Alkawari da samun Ganima me yawa bayan sun dawo daga Hudaibiyya -itace Ganiman Khaibara- dacewa kuma ze gagauto masu da ita kuma sune zasu sameta ba wasunsu ba, kuma Munafukai zasu ce zasu raka su, kuma Musulmi zasu ce bazaku tab’a binmu ba, kuma zasu cije se sun sauya maganar Allah, kuma zasu ce wa Muminai kawai kunayi mana Hassada ce, kuma Allah yabasu Amsa da cewa

( Sun kasance basa iya Fahimta se Y’an kad’an) Sur. AlFathi-15.

Sannan kuma Alk’ur’ani yabada wannan Labarin gaba dayansa ga Muminai Lokaci- zuwa Lokaci Mataki – Mataki, Kalma da Kalam.

To a nan zamu riski bam-bamcin dake tsakanin wadanda suka had’a rayuwansu suka daureta da Alk’ur’ani, kuma suka Fuskanceshi suna karantashi, suna Haddace shi, suna Karanta Fassaran shi-wato Tafsirinsa-, suna Yin Tadabburinsa –wato Yin Tunani acikin ayoyinsa-,da Umarnin Alk’ur’ani suke aikata komai, kuma gareshi suke komowa, da Wanda ya sanya zantukan dan Adam sunesukafi damunshi da abinda yake shagaltar dashi. Ya Kaicon wadanda suke Neman Ilimi suna ba Alk’ur’ani da Tafsirinsa kaso me yawa na laokutansu na Karatu. Akwai cigabansa nan gaba insha Allahu a kashi na biyu.