MARABA DA ZUWA SHAFINMU NA MUSULUNCI

31 Dec 2007

TARE DA MANZAN ALLAH SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM NA (1)

HAIHUWAR MANZAN ALLAH SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM

1. Allah Madaukakin Sarki Yace:. ( Hakika Allah yayi baiwa akan Muminai da ya aiko da manzo daga cikinsu, yana karanta masu Ayoyinsa, kuma yana tsarkakesu, kuma yana karantar dasu Littafi -wato Alk'ur'ani da Hikma -watom Hadisi, duk da sun kasance kafin hakan suna cikin bata a bayyane) S. Al'imaran-164.

2. kuma madaukakin Sarki yace: ( kace masu nifa mutum ne kamanku, anayimini wahayi cewa tabbas mahaliccinku shine ubangiji guda daya) S. kahf-11.

3. An tambayi Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam gameda Yin Azumin Ranar Litinin?

Yace: " wannan rana ce da'aka haifeni a cikinta, kuma a cikinta aka aikoni, kuma a cikinta aka saukar min da Alk'ur'ani" Muslim

4. Hakika an haifi Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam a Ranar Litinin cikin watan Rabi'ul Awwal a Makka, a shekaran Fil- wato Giwa. shekara ta 571 C.E. daga Iyaye biyu sanannu: Mahaifinsa shine ABDULLAHI dan Abdulmutallib, Mahaifiyarsa kuma itace AMINA yar Wahabu, kakansa yarada masa suna MUHAMMAD Sallallahu Alaihi Wasallam, kuma Mahaifinsa ya rasu kafin Haihuwarsa.

5. Lallai Yana daga cikin Abubuwan dasuke wajibi akan Musulmai shine su san darajan wannan Manzo me girma, kuma suyi hukunci da Alkur'ani da'aka saukar masa, kuma su dabi'antu da halayensa kuma su bada kokari wajen kira zuwaga Tauhidi-kadaita Allah- wanda akansa yafara...........................me bin Umarnin Allah Madaukakin Sarki: ( Kace ina kira zuwaga Ubangijina kuma bazana hadashi da kowa ba cikin bauta). Sur.Aljinn-20.