MARABA DA ZUWA SHAFINMU NA MUSULUNCI

6 Aug 2007

Shi yasa aka fifitasu....

Dasunan Allah mai Rahama mai Jinkai WADANSU ABUBUWA DA'AKA KEBANCE AL'UMMAR MUSULMI DASU AKAN SAURAN AL'UMMU Hakika Allah madaukakin Sarki ya karrama A'ummar musulunci, kuma ya daukakata akan sauran al'ummu, ya kebanceta da wasu abubuwa, ita kadai. Tabbas tasami wannan girmane, saboda daraja da falalan Annabinta Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam, da imani datayi dashi. Daga cikin daukakashi da Allah yayi bayan yazabeshi daga cikin halittu,ya zaba masa Abokai (wato sahabbai) matemaka agareshi. Allah madaukakain Sarki yace ( "shine wanda yazabeku –sahabbai- kuma be sanya maku wani abu me wahala acikin Addini ba" ) (Sur. Hajji -78.) kuma yace ( "kuma haka muka sanyaku Al'umma mafificiya domin kuzamo masu sheda ga mutane (Annabawan dasuka gabata akan mutanensu) kuma manzo yazama me shesa akanku….") Sur. Baqarah-143). Saboda haka ne yazama dole akan muslmai dasusan abinda suke ciki na ni'ima,da kuma abinda suke akai na alkhairi, don suyi rikoda shi kumasuyi rikodashi kuma suyi aiki domin yadashi……………………….zamu cigaba insha Allah

4 Aug 2007

MATSAYIN SALLAH

Dasunan Allah Mai Rahama Mai Jinkaiِ
SALLAH
Ita Dayace daga cikin rukunnan musulunci guda biyar, wanda Allah maduakakin sarki ya wajabtata guda Hamsin(50) yayin da manzan Allah Sallallaahu Alaihi Wasallama yaje Mi'iraaji (wato Sama) yakarbo ta yayi ta neman ubangiji da ya ragemana ita har aka rageta zuwa guda biyar (5) kamar yadda take a yau saboda tausayin manzan Allah garemu Sallalahu Alaihi Wasallam. Kuma manzan Allahn Sallalahun Alaihi Wasallam yace "Itace farkon abinda za'ayi Wa bawa sakamako (hisabi) Ranar k'iyama Idan tayi kyau dukkan Sauran aiki zasuyi kyau bawa yasama tsira kuma idan tayi muni to dukkan sauran ayyuka bazasu amfane bawaba. Sannan kafin Sallar da bawa yakeyi tasami karbuwa se idan tadace da yadda manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yayita kuma ya karantar domin fadan Ma'aiki "Kuyi Sallah Kamar yadda kuka ina yin Sallah", Sannan an wajabta yinta acikin jama'a (wato Jam'i a masallaci). Kuma wanda duk yabarta to yabar musulunci kamar yadda ma'aiki Tsira da Amincin Allah su kara Tabbata Agareshi yace " Alkawarin dake tsakaninmu dasu shine Sallah duk wanda yabarta to ya kafirta". To idankowannan shine al'amarin Sallah to yazama dole akan kowane muslmi dayasan mecece Sallah? Kuma menene Hukunce-Hukuncenta? da abubuwan dasu batata domin ta kasancce karbabaiya a wajen Allah Madaukakin Sarki…………….

MABUDI

Dukkan yabo da Godiya sun tabbata ga Allaah madaukakin sarki Tsira da Amincin Allaah su kara tabbata ga manzan Allaah da Iyalan gidansa da duk wadanda suka bi karantarwarsa wato sunnarsa har zuwa ranar sakamako. Amin

23 Jun 2007

BAYANAI GAMEDA SHAFIN

Bismillahir Rahmanir Raheem Muna maku maraba da shigowa wannan Shafi namu na musulunci, wanda zekawo maku, bayanai akan abinda yashafi Rukunnan Musulunci guda biyar, wato Kalmar Tauhidi, Dallah Azumi Zakka da Hajji. Sannan daga baya zamu bayani akan abinda yashafi Mu'amala, kama daga kasuwanci, Hayaa da Auratayya, Zamantakewa da makwabtaka da.......... tareda yin bayani akan Hukunce Hukuncensu a musulunci, tareda kawo dalilai daga cikin Littafin Allah da Sunnar Manzan Allah Sallallahu Alaihi WASAllam, da zantukan dasuka Inganta na Malamai, domin sanarda musulmi wanda yake Bahaushe ko wanda iya karantun Hausa, bayanai masu inganci gameda Addininsa. Sannaan kuma munaso mu dinga kawo maku fatawa ta malamai a cikin gida najeriya ko a wajenta. ALLAH MUKE ROKO DA YAYI MANA JAGORANCI aMIIIIIIIIIIIN.