MARABA DA ZUWA SHAFINMU NA MUSULUNCI

20 Jul 2008

SIFFAR BARCIN MANZAN ALLAH SALLALLAHU WASALLALAM

SIFFAR BARCIN MANZAN ALLAH SALLALLAHU WASALLALAM

  • Ya kasance yana Barci a Farkon dare, ya raya karshensa – wato yanayin Sallah a cikinsa kenan- Bukhari da Muslim.

Ø Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam Ya Kasance idan ya hau kan shinfidarsa zeyi Barci yana cewa : “ Bismikallahumma Amutu Wa’ahyaa” (Ma’ana Da sunanka Ubangiji, nake Mutuwa kuma nake Rayuwa. Mutuwa = Yin barci , Rayuwa = Farkawa daga barci) kuma idan ya farka daga barci yana cewa “ Alhamdu lil lahil ladhi Ahyaana ba’ada ma Amaatana Wa ilaihin nushur” ( Ma’ana Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Wanda ya Rayamu bayan ya kashe mu, kuma gareshi tashi yake) Muslim.

Ø Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Ya Kasance idan ze kwanta barci yana sanya tafin Hannunsa na dama kar-kashin kuncinsa na dama se Yace: “Rabbi Qini azabaka Yauma tab’athu ibadika” (Ma’ana Ya ubangiji ka tsareni daga Azabarka ranar da zaka tashi bayinka –wato ranar Lahira kenan) Tirmidhi .

Ø Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam Ya Kasance a kowani dare idan ze kwanta yana hada tafukan Hannayensa se ya huresu Ya karanta (Kulhuwallahu Ahad) da (Kul’a’uzu birabbil Falaq) da (Kul’a’uzu bi rabbin Nas), sannan ya shafama inda ya sauwaka a jikinsa, yana farawa da kansa se fuskarsa da barin gaba na jikinsa, yana yin hakan sau uku. Bukhari da Muslim.

Ø Ya Kasance yana barci a kan matashin kai (pillow) na Fata cikinsa an cikashi da gashin bishiyar dabino Ahmad.

Ø Shimfidar da Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Ya Kasance yana barci akanta ta Fata ce da aka cika da gashin bishiyar dabino Muslim.

Ø Nana Aisha Allah ya kara Yarda agareta tace Ya Manzan Allah Shin kana barci ne kafin kayi Sallar Witri? Se Yace: “ Yake Aisha: Idanuwana suna Barci amma Zuciya ta bata Barci” Bukhari da Muslim.

1 May 2008

NA UKU (3)

NA BIYAR: AMBATON ALLAH (WATO YIN ZIKIRI)

Ambaton Allah yana daga mafi girman dalili na samun Tabbatuwa.

Kayi tunani akan kusanci da juna da umarni guda biyu sukayi cikin Fadinsa madaukakin Sarki : [ Yaku Wadanda sukayi Imani Idan kun hadu da wata Jama’a – wato kafirai kenan a Yaki – To ku tabbatu, kuma ku ambaci Allah da yawa…] [Sur. Al-anfal- 45]. Ya sanya Zikiri a matsayin mafi girman abinda yake temakawa wajen tabbatuwa a fagen Jihadi.

“ Kuma kayi tunanin Rumawa da Farisawa a Yakukan da’akayi da kuma Masu Zikiri duk da Karancinsu.

Sannan da Menene Annabi Yusuf (Alaihis Salam) Ya samu Tabbatuwa sanda Fitinar Matannan me mulki da tsananin Kyawo ta nemeshi akanta? Shin be shiga cikin Ganuwan (Ma’azal lah) ba Ma’ana Ina neman kariya daga Allah kuma shin rundunar Sha’awa bata bal-balce ba akan katangan da suke kareshi?.

To hakane Yin Zikiri yake aiki wajen Tabbatar da Muminai.

HANYOYIN TABBATUWA NA UKU (3)

NA SHIDA: MUSULMI YAYI KWAɗAYIN BIN INGANTACCEN TAFARKI

Ingantaccen tafarki ƙwãya ɗaya tal, daya zama tilas kowani musulmi yabi, shine: tafarkin Ahlus-sunnah wal-jama’a. tafarkin Jama’a da’aka temaka, kuma Jama’a ne tseratattu, mãsu tsabtatattan Aƙida, da manhaji ingantacce, da bin Sunna da dalili, da banbanta daga maƙiyan Allah, da rabuwa da masu ɓata.

Idan kuma har kanã so kasan matsayin bin ingantaccen tafarki, a wajen tabbatuwa, to kayi tunani, kuma ka tambayi kanka: Me yasa dayawa daga cikin wadanda suka gabãta da wadanda suka biyo bãyansu suka halaka, kuma suka ruɗe, duga-dugansu suka kãsa tabbata akan tafarki madai-daici? kuma basu mutu akansa ba? Ko kuma A’A sun isa zuwa gareshi bayan sun ƙãrar da mafi yawan rayuwarsu, kuma sun ɓatar da mafi tsãdan lokutansu a cikin rayuwansu?.

Zakaga ɗayansu yana ta yãwo, a cikin masaukai na bidi’a da ɓata, daga Falsafa zuwa ga ilimin kalami wato zance, daga Mu’utazilanci zuwa ga Tahrifi da tãwili zuwa tafwidi zuwa ga Murji’anci, daga wata darik’a cikin Sũfanci zuwa wata.

To haka Y’an bidi’a, sũma sunã da rũɗu, da rashin natsuwa, ka duba kaga yanda aka hanãma Y’an Zance (wato Ahlul kalam) tabbatuwa a lokacin mutuwa, magabata Sukace: “Wanda sukafi kõwa Shakka a lokacin mutuwa sune Y’an Zance (Ahlul kalam)”.

Sedai kayi tunani kaga, shin akwai koda mutum ɗaya daga cikin Ahlus Sunna wal-jama’a, da yataɓa barin tafarkinsa, ya ƙyamaceshi, yayi fushi dashi, bayan yã bishi, yã sanshi, yã fahimceshi? Zata yiwuwa, Mutum ya barsa Saboda son rai, ko dan kwaɗayin abin duniya, ko saboda Shubuha da’aka bijiroma hankalinsa me rauni da’ita, Amma baya barinsa, saboda wai yaga wani tafarkin da yafishi inganci, ko yagãno cewa shi ɗin ɓatane.

Kuma abinda ze gaskata hakan shine: Lokacin da Hiraƙal ya tambayi Abũ Sufyan, gameda mãsu bin Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallamr, Se Hiraƙal Yace ma Abũ Sufyan: “Shin a cikinsu akwai koda Mutum ɗaya da yataɓa yin RIDDA -wato ya fita daga Addinin-, ya yi fushi dashi ya ƙyamace shi, bayan ya shiga cikinsa?” Se Abũ Sufyan Yace: A’a se Hiraƙal Yace: To hakanan Imãni yake, idan ya cakuɗa –wato ya haɗu- da Zũciya”.

Sau dayawa Munji cewa Shugabanni sun bar Masuaki na Bidi’a, wasu kuma Allah ya shiryasu, sun b’ar ɓata sun koma zuwa ga Mazhabin Ahlus Sunna Wal-jama’a, suna masu nuna ƙyama da fushi ga tafarkin da suke a kansa na farko,

Shin ko mun taɓa jin Akasin hakan?!

To idan har kanã son tabbatuwa, to wãjibi ne kabi tafarkin Muminai.

NA BAKWAI: TARBIYYA:

Tarbiyya ta Imãni da ilimi da fahimta, wanda take akan mataki - mataki, Ma’auni ne daga cikin ma’aunan Tabbatuwa.

TARBIYYAN IMANI: Itace take kãre zukãta da rãyuka. kuma Ana samun ta ne ta hanyar Jin tsoron Allah, da fãta, da Soyayya, wandu suke kõre bũshewar zuciya, sakamakon yin Nisa da Nassosin Alƙur’ani da Hadisan Manzan Allah Sallallahu Alihi Wasallamr, da durƙusãwa ga Zantuttukan Mazaje.

TARBIYYA TA ILIMI: Itace wacce take tsaye akan dalili ingantacce, wanda take kõre yin taƙalidanci da ….makoma…. abin zargi.

TARBIYYA TA FAHIMTA: Itace wacce da ita zãka san tafarkin mãsu laifi (mujurimai), da karanta Shirye-Shiryen maƙiya Musulunci, kasan abubuwan da suke fãruwa a gefenka, ka fahimci abubuwan dasuke fãruwa, dan ka iya yin hukunci akansu, Hakan ze kõre maka dõɗewa da zama a wuri ɗaya da rashin fita daga cikin bi’a da take Y’ar karama Iyakantacciya.

TARBIYYAN MATAKI-MATAKI: Itace Wacce zatabi da Musulmi da kaɗan da kaɗan (da sannu da sannu), har ta ɗagãshi zuwa ga matakin da ze cika, da tsari dai-daitacce, wanda hakan ze kõre masa Yin gaggawa da sauri da tsallake, wanda yake ruguzawa.

Kuma domin mu san mahimmancin wannan gaɓan cikin sassan tabbatuwa, to se mukoma zuwa ga Tarihin Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasllamr, kuma muyiwa kawunanmu tambaya?

**Menene asalin abinda ya tabbatar da Sahabban Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, a lokacin da’ake gãna masu Azãba?

** Me yasa Bilãl da Khabbab da Mus’ab da Ãlu Yãsir da sauransu, daga cikin masu rauni, kai har Manyan Sahabbai sũma a killacewan da’akayi musu a Bani Shi’ab da sauransu?.

** Shin zeyiwu tabbatuwansu ta kasance ba tãre da wata Tarbiyyaba me zurfi ba daga Fitilan Annabta, wanda ta tarbiyyantar da rãyukansu?

Mu ɗauka wannan Sahabin ƙhabbãb binil Art t Allah yakãra Yarda a gareshi, wanda Shugabansa ta kasance tana ƙõna wayã, irin wanda ake gasa nãma dashi, har se tayi Jãjur, sannan se ta ɗõra bayansa akai –wato tana gasa bayansa kaman nãma kenan a bũɗe –, Kuma Mai dake fitõwa daga bayansa ne, idan ya kwararo, yake kasheta. To Me yasa yayi haƙuri akan haka?

Bilãl Kuma yana cãn ƙarƙashin dũtse a kan Sahãra, SUMAIYA kuma tana ɗaure cikin Mari. Gawata tambaya da’aka samu a Lokacin dasuke Madina: Su wãnene suka tabbata tãre da Manzan Allah Sallallanu Alaihi Wasallam r a Yaƙin Hunãin lõkacin da aka sãmu Nasara akan dayawa daga cikin Musulmai? Shin Sãbabbun Musulunta ne, ko wanda suka musulunta a Yãƙin Makka, wanda basu sami isasshen lõkaci na tarbiyya ba a Makarantar Annabta, wanda dayawa daga cikinsu sun fita ne saboda neman Ganima? A’a...Mafi yawa cikin waɗanda suka tabbata sune: waɗannan zãɓaɓɓun Muminan, da suka sãmu adadi me girma na Tarbiyya daga wajen Manzan Allah Sallallanu Alaihi Wasallam r . Ba domin akwai Tarbiyya ba, Shin kãna ganin waɗannan Sahabban zãsu tabbata?

TAMBAYA : Hadisin dayake cewa “ Kada kuyi Azumi ranar Asabar Face abinda aka Farlanta maku – wato Ramadan –“ shin Hadisin Ingantacce ne, kuma menene ma’anar Hadisin kuma shin ya kunshi dukkan Azumi ne?

ME BADA AMSA: Shaikh Abdur rahman bin Jibrin Mamba a cikin Majalisar manyan malamai masu fatawa a kasar Saudi Arabia.

AMSA: an kebance ranar Asabar ne da Hani saboda yahudawa sun kasance suna barin aiki a cikinta, se aka hana girmama ranar saboda kada ayi kamance – ceniya dasu, kuma ya halarta a Azumce Asabar idan akwai sababi, Kaman wanda yake Azumi rana ya sha ruwa rana, haka idan yayi dai- dai da ranar Arafa, ko Ranar Ashura da makamantansu, Ma’anar (abinda aka Farlanta maku) ma’anarsa aka shar’anta, kuma aka sunnanta maku.

23 Mar 2008

SHIN KE MACE CE ME KAMA DA MAZA WAJEN KOKARI?! GA WASU HANYOYI GUDA GOMA ‎DOMIN KIZAMA HAKAN

Abune dayake sananne cewa kina fuskantar matsaloli cikin ranki da kuma zamantakewa a wajen kulla Alaka da aikace - aikacenki, to abinda yakamata kisani shine rayuwa bata rabuwa da wadannan matsalolin, kuma babu shakka nasan cewa sau dayawa kin yi tunani akan wata matsala da ta faru dake, bayan kin dauka mataki domin kiga shin kinyi dai dai koko shin kin yi kuskure? akan matakin dakika dauka, daganan kina kara samun kwarewa wajen magance matsalolinki, ba’a baukatan koda yaushe kizama me ran karfe wajen war - ware matsaloli, amma ga wasu abubuwa dazasu temaka maki wajen hakan

  1. Kiyi abinda ake kira jeranta abubuwa gwargwadon muhimmancin su wato (First thing First) kuma ki tsara ayyukanki,, hakan ze kareki daga damuwa, saboda kina zartar da abinda yakeda muhimmanci sosai, kuma ze rage maki damuwa, saboda ayyukan da bakiyi su ba, basu da muhimmanci sosai.
  2. Kada ki dora ma kanki abinda yafi karfinki, Allah Madaukakin Sarki yace: (La yukallifullahu nafsan illa wus aha Suratul Bakara 286. Ma'ana Allah baya kallafa ma rai face abinda take iyawa. To ya tausaya mana saboda haka yakamata mu tausaya ma kawunanmu, amma batare da kasala ba ko rashin yin aiki, kuma kada kice se kinyi komai da kikeso, wato ki cika komai, domin cika na Allah ne kadai, takenki yazama “Adai daita sahu”
  3. Kada ki shagaltu da aiki fiye da daya, a lokaci guda domin ze kasa hankalinki biyu da kokarin dakikeyi, daga nan baza ki iya yin aiki kwakkwara ba me aminci, abinda yakamata shine: ki kammala wani sannan ki fara nagaba dashi, domin hakan ze saki jin dadi da jin cewa kina samun nasara a rayuwa, kuma ze sa kiyi kwadayin aiwatar da wani aikin.
  4. Wajen alakar ki da sauran jama’a kuma: kiyi kokari ki fuskance su da rashin yin karya kuma bada barin gaskiya ba, A’a cikin natsuwa da hankali, kuma kada kiyi fushi, idan wasu basuyi kawance dake ba, haka kuma ki karbi kuskure idan anyi maki gyara, sawa’un daga kawayenki ne ko wasu daban, ki dauki hakan a matsayin jarrabawa na fadada kirjin ki (wato koyan yin hakuri).
  5. kada kibar jarabawa da baki samu nasara ba akanta, ta hana ki aiwatar da wani aiki, yin tunani akan abinda baki samu nasara ba akansa zesa kiyi wanda yafishi kyau, abinda ya kamata ki dauki rashin samun nasaranki a matsayin ma’auni na samun darasi da kwarewa. Ba matsayin tsoro ba.
  6. Wajen alakanki da sauran jama’a, ki dinga kokarin yawan mur mushi, kuma ki tuna da hadisin da ke cewa “ Yin mur mushin ka ga dan uwanka SADAKA ne" – (wato akwai lada a cikinsa) kuma ki sani dariya na kara maki soyayya dake sa zuciya ta natsu, kuma kiyi kokarin yin Magana da sauti dan kadan domin daga sauti na kara rashin jituwa.
  7. Likitoci suna cewa: Cakuda jiki yana temakawa wajen rage rashin natsuwa da damuwa, To saboda haka ki kwatanta kigani, musamman wajen wanka, da lokacin alwala ki dinga caccakuda yatsun hannu da na kafa.
  8. Ki yi kokari ki dinga yin Zikirin Safiya da na Marece, ze saki a koda yaushe kizama kina tareda Allah, kuma ze kara maki jin cewa Allah yana ganinki a koda yaushe, kuma kina cikin Kariyarsa, kuma kina da ikon ketare kowani abu dayake da wahala, da war - ware matsaloli da datarwansa (ikonsa), ki rokeshi dacewa, da yin dai - dai, Shi Allah yana yaye bakin ciki, kuma yana amsan rokon wanda ya kirasa (mabukaci).
  9. Kada ayyuka ko damuwa susa ki dinga jinkirta sallah, SALLAH hutu ce ga rai kuma natsuwa ce ga zuciya, Kuma Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya kasance yana cewa “Bilal ka hutar damu da Sallah” lokacin da zece ya tada ikama.
  10. Kada kiyi kokarin Boye rashin jin dadinki da damuwanki, A’a kiyarda cewa kinada damuwa, amma ki amince cewa kina da ikon da zakiyi nasara akansa, kuma idan kikaji cewa kinaso kiyi kuka, to kada kiyi kokwanto kiyi kuka da hawaye domin yin kuka ba dalili ne na rashin iko ba ko shi ke nuna kina da rauni, a’a kuka hanya ne na rage damuwa da rai ke ciki.

20 Mar 2008

HUKUNCIN SHAN TABA DA WIWI

Shan Taba ko Wiwi da makamantansu abubuwane da Addinin Musulunci ya haramta ga dalilai akan haka :- Fadin Allah Madaukakin Sarki : ( Kada ku kashe kawunanku, Lallai Allah mai jinkai ne akanku ) da Fadinsa : ( kuma kada ku jefa hannayenku zuwaga hallaka) wato kada kuyi duk abinda zezama sanadiyyar hallakanaku, kuma likitoci sun tabbatar da cewa Shan taba da Wiwi suna cutarwa, saboda haka abinda yake cutarwa haramun ne. ga wani dalilin kuma Allah Madaukakin Sarki Yace: ( kuma kada kuba wawaye dukiyoyinku wanda Allah yabaku) Ya hana muba wawaye kudadenmu saboda suna lalatardasu da bannatawa, kuma babu shakka sayen taba da wiwi barnan kudine, kuma yana cutar da mai sha d a kuma wanda yake shakan hayakin, kuma ance wanda yake shaka yafi cutuwa akan me shan, kaga kenan laifi biyu ne, na farko cutar da kai da ayoyin baya suka hana, na biyu cutar da waninka da shima Addini ya hana. Saboda haka aka haramta shan taba da wiwi da dalilin hanin wancan ayan da kuma Fadin Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya hana wulakanta kudi, Yace: ( babu cuta kuma babu cutarwa) kuma shan wadannan abubuwa na samarda cutarwa, kuma in mutum yasaba dasu, yanada wahala ya iya barinsu , idan be same suba yana samun kunci cikin ransa, kai duniya matayi mai kunci, kaga ko wannan ya isheshi fitina. Allah ya karemu.

13 Feb 2008

NA FARKO: FUSKANTAR ALQUR’ANI: .