NA SHIDA: MUSULMI YAYI KWAɗAYIN BIN INGANTACCEN TAFARKI
Ingantaccen tafarki ƙwãya ɗaya tal, daya zama tilas kowani musulmi yabi, shine: tafarkin Ahlus-sunnah wal-jama’a. tafarkin Jama’a da’aka temaka, kuma Jama’a ne tseratattu, mãsu tsabtatattan Aƙida, da manhaji ingantacce, da bin Sunna da dalili, da banbanta daga maƙiyan Allah, da rabuwa da masu ɓata.
Idan kuma
Zakaga ɗayansu yana ta yãwo, a cikin masaukai na bidi’a da ɓata, daga Falsafa zuwa ga ilimin kalami wato zance, daga Mu’utazilanci zuwa ga Tahrifi da tãwili zuwa tafwidi zuwa ga Murji’anci, daga wata darik’a cikin Sũfanci zuwa wata.
To haka Y’an bidi’a, sũma sunã da rũɗu, da rashin natsuwa, ka duba kaga yanda aka hanãma Y’an Zance (wato Ahlul kalam) tabbatuwa a lokacin mutuwa, magabata Sukace: “Wanda sukafi kõwa Shakka a lokacin mutuwa sune Y’an Zance (Ahlul kalam)”.
Sedai kayi tunani kaga, shin akwai koda mutum ɗaya daga cikin Ahlus Sunna wal-jama’a, da yataɓa barin tafarkinsa, ya ƙyamaceshi, yayi fushi dashi, bayan yã bishi, yã sanshi, yã fahimceshi? Zata yiwuwa, Mutum ya barsa Saboda
Kuma abinda ze gaskata hakan shine: Lokacin da Hiraƙal ya tambayi Abũ Sufyan, gameda mãsu bin Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallamr, Se Hiraƙal Yace ma Abũ Sufyan: “Shin a cikinsu akwai koda Mutum ɗaya da yataɓa yin RIDDA -wato ya fita daga Addinin-, ya yi fushi dashi ya ƙyamace
Sau dayawa Munji cewa Shugabanni sun bar Masuaki na Bidi’a, wasu kuma Allah ya shiryasu, sun b’ar ɓata sun koma zuwa ga Mazhabin Ahlus Sunna Wal-jama’a, suna masu nuna ƙyama da fushi ga tafarkin da suke a kansa na farko,
Shin ko mun taɓa jin Akasin hakan?!
To idan
NA BAKWAI: TARBIYYA:
Tarbiyya ta Imãni da ilimi da fahimta, wanda take akan mataki - mataki, Ma’auni ne daga cikin ma’aunan Tabbatuwa.
TARBIYYAN IMANI: Itace take kãre zukãta da rãyuka. kuma Ana samun ta ne ta hanyar Jin tsoron Allah, da fãta, da Soyayya, wandu suke kõre bũshewar zuciya, sakamakon yin Nisa da Nassosin Alƙur’ani da Hadisan Manzan Allah Sallallahu Alihi Wasallamr, da durƙusãwa ga Zantuttukan Mazaje.
TARBIYYA TA ILIMI: Itace wacce take tsaye akan dalili ingantacce, wanda take kõre yin taƙalidanci da ….makoma…. abin zargi.
TARBIYYA TA FAHIMTA: Itace wacce da ita zãka san tafarkin mãsu laifi (mujurimai), da karanta Shirye-Shiryen maƙiya Musulunci, kasan abubuwan da suke fãruwa a gefenka, ka fahimci abubuwan dasuke fãruwa, dan ka iya yin hukunci akansu, Hakan ze kõre maka dõɗewa da zama a wuri ɗaya da rashin fita daga cikin bi’a da take Y’ar karama Iyakantacciya.
TARBIYYAN MATAKI-MATAKI: Itace Wacce zatabi da Musulmi da kaɗan da kaɗan (da sannu da sannu),
Kuma domin mu
**Menene asalin abinda ya tabbatar da Sahabban Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, a lokacin da’ake gãna masu Azãba?
** Me yasa Bilãl da Khabbab da Mus’ab da Ãlu Yãsir da sauransu, daga cikin masu rauni,
** Shin zeyiwu tabbatuwansu ta kasance ba tãre da wata Tarbiyyaba me zurfi ba daga Fitilan Annabta, wanda ta tarbiyyantar da rãyukansu?
Mu ɗauka wannan Sahabin ƙhabbãb binil Art t Allah yakãra Yarda a gareshi, wanda Shugabansa ta kasance tana ƙõna wayã, irin wanda ake gasa nãma dashi, har se tayi Jãjur, sannan se ta ɗõra bayansa akai –wato tana gasa bayansa kaman nãma kenan a bũɗe –, Kuma Mai dake fitõwa daga bayansa ne, idan ya kwararo, yake kasheta. To Me yasa yayi haƙuri akan haka?
Bilãl Kuma yana cãn ƙarƙashin dũtse a