MARABA DA ZUWA SHAFINMU NA MUSULUNCI

28 Feb 2009

HADA ALAH DA WANI (SHIRKA)

SHIRKA

Shirka itace mafi girman abinda Allah ya haramta aayan kasa , Saboda Hadisin da Abi Bakrata ya ruwaito Yace : Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam: "Shin bana baku labarin mafi girman Manyan laifuka ba har sau uku Se Sahabbai sukace bamu ya Manzan Allah , se Manzan Allah Yace: Shine Yin Shirka da Allah…" Bukhari No. 2511.

Haka kowani laifi Allah ze iya gafartawa me shi in banda Shirka domin ita se anyi mata tuba kebantatta Allah Madaukakin Sarki Yace: ( Lallai Allah Madaukakin Sarki baya yin gafara ga wanda yayi Shirka dashi , amma yanayin gafara ga abinda ba Shirka ba ga wanda yaso ) Sur. An Nisa'i – 48.

Kuma daga cikin Nau'ukan Shirka , akwai Shirkan da take fitar da mutum daga Musulunci , kuma me ita ze dauwama a cikin Wuta matukar ya mutu yana aikatawa.

Kadan daga cikin wannan Shirkan data watsu a garuruwan Musulmi akwai :- Yin Bauta ga Kabari…...

YIN BAUTA GA KABARI

Kudurin cewa Waliyyan da suka mutu suna biyan bukatu , kuma suna faranta bakin ciki , da neman temakonsu da neman cetonsu , Allah Madaukakin Sarki Yana Cewa: (Kuma Ubangijinka yayi hukunci cewa kada ku bautama wani inbanda shi) Sur.Al'isra'I – 23. haka kuma kiran Annabawa da Mutanen kwarai dasuka mutu ko waninsu dominsu cecesu , ko su kubutar dasu daga tsanani. Bayan Allah Madaukakin Sarki Yana cewa: (Wanene wanda yake amsaa ma mabukaci idan yakirashi , kuma yake yaye bakin ciki , kuma ya sanya ku halifofi akan kasa, shin akwai wani abin bauta in banda Allah?) Sur. Naml -62.

Wasunsu kuma zasu riki sunan wani Shehi ko Waliyyi idan zasu tashi ko zasu zauna ko idan sunyi tuntube ,kuma duk sanda suka cikin wani hali na bala'I ko bakin ciki , se kaji wannan yana cewa Ya Muhammad! , wancan sekaji yana cewa Ya Aliyyu ! , ko Ya Husaini! , ko wancan YAce Ya Badawi ko Ya Jilani , wannnan na fadin Ya shazali! , ko ya Rufa'I , wani kuma na kiran Ya Saidarus! Ko Ya Saiyada Zainab , wani kuma na kiran dan Alwan bacin Allah madaukakin Sarki Yana Cewa: ( Lallai wadannan da kuke kira Wanda ba Allah ba bayi ne kamanku) Sur. Al'a'araf – 194.

Wasu kuma da suke bauta ma Kabari zakaga suna kewayashi –wato suna masa dawafi- kuma kaga suna sumbantan rukunnansa kaga suna shafe jikinsu dashi , kuma suna smbantansa, kuma sun abaca baca da kasa a fuskokinsu , kuma suna makabarin sujjada , kaga sun tsaya a gabansa suna masu cike da tsoro da kaskantar dakai suna rokon biyan bukatunsu , na neman warkar da mara lafiya , ko neman Haihuwa ko sauwake wani abu , kai zakaji wani ma yana kiran wand ke cikin kabari yana cewa Ya Sayyidi - wato Shugabana- nazo maka daga gari me nisa kada ka bani kunya. Allah Madaukakin Sarki kuwa Yana Cewa: ( Shin wanene yafi bata fiye da wanda ya kira wani wanda ba Alah ba , wanda baya karba masa har zuwa tashin Alkiyama , kuma alhali su rafkanannu ne gameda rokonsu da'akeyi musu) Sur. Al'ahkaf – 5. Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Yace: " Duk wanda ya mutu alhali yana rokon wani wanda ba Allah a matsayin kishiya ze shiga Wuta" Bukhari. Wasu daga cikinsu zakaga suna aske gashin kawunansu a wurin kabur-buran , wani daga cikinsu ya wallafa Littafi ne me taken (Manasiku Hajjil Mashahid) Ma'ana Ayyukan Hajjin Kabur – bura na Waliyyai kenan , wasu kuma suna da Kudurin cewa Waliyyai sunayin tasarrufi a duniya wato suna zartar da wasu abubuwa dake faruwa , suna Cutarwa suna amfanarwa Alhali kuwa Alah Madaukakin Sarki Yana cewa: (Kuma idan Allah ya sanya maka wani Ciwo to babu me yaye maka in bandashi kuma idan yayi nufinka da wani Alkhairi to babu me mayar da Wannan Falalar) Sur. Yunus – 107.

Kuma Yana daga cikin Shirka Yin Alwashi ga wanda ba Allah ba kamar yanda wasu sukeyiwa wasu kabur bura awashi. Allah ya Shiryamu.

zamu cigaba insha Allahu.

*** Yana daga cikin Babban Shirka Yin Yanka ga wanda ba Allah ba , Allah Madaukakin Sarki Yana cewa : (Kayi Sallah ga Ubangijinka ka kumayi Yanka) Sur. Alkauthar -2. abin nufi kayi yanka dan Allah kadai kuma da sunansa , Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Yace: " Allah ya La'anci wanda yayi Yanka ga wani wanda ba Allah ba" Imamu Muslim.

Kuma aikata haramun guda biyu zasu iya haduwa ga abin Yanka sune: Yin Yanka badan Alah ba , sannan YinaYankan bada sunan Allah ba , kuma dukansu abubuwa ne dasuke hana cin Yanka. Kuma akwai Yanka na Jahiliyya wanda ya watsu a zamanin mu shine " Yin Yanka saboda Aljanu" sun kasance idan suka saya gida ko suka gina gida ko suka haka rijiya se suyi Yanka a wajen ko akan kofar gidan ko rijiyar domin tsoron cutarwar Aljanu