MARABA DA ZUWA SHAFINMU NA MUSULUNCI

29 Nov 2007

ABUBUWAN HANI A CIKIN HAJJI

ABUBUWAN DA AKA HARAMTASU GA MAHAJJACI

Duk wanda yayi Harama da Hajji ko Umurah an haramta masa, abubuwan da suke zuwa: 1.Rufe kai ga na miji, domin haramarsa itace bude kai, haka kuma Rufe fuska da Hannaye ga mace, domin haramarta itace budesu, sedai idan zata wuce maza, to seta rufe fuska. Kuma idan daya daga cikinsu yarasu, to za’a rufeshi a cikin haraminsa, se abude fuskar maace, kuma a bude kan na miji, kuma baza’a samasa turare ba.

2. Aske gashin kai ga na miji.

3.Yanke kumba.

4. Sanya Turare, sedai abinda yake a tufafinsa, wanda yayi harami dashi to babu laifi akansa.

5.Sanya tufafi dunkakke.

6. yin Jima’I da abubuwan dasuke haifar dayinsa.

7. Yin farautan wani abu, ko temaka ma meyin hakan, ko cin abinda akayi farautarsa.

8. Yayi tad’i wato neman aure, ko daura masa aure, ko aurarwa waninsa, ko ya halarci daurin auren waninsa.

WAR-WARE AIKIN HAJJI KARAMA DA BABBA

Mahajjaci yanada war-wara guda biyu: Karama shine bayan jifan jamratul ak’aba –wato shedan babba- a ranar Idi kenan, to daga nan komai ya halatta ga mahajjaci hatta saduwa da Iyali. da kuma War-wara babba, wanda yake bayan dawafin Ifada.

FIDIYA GA WANDA YA AIKATA ABINDA AKA HARAMTA

Duk wanda ya aikata daya daga cikin abubuwa guda biyar na farko da’aka haramta masa, da gangan –wato-yana sane bada mantuwa ba- to akwai fidiya akansa, kuma yanada zabi a cikin hakan, kodai ya yanka dabba, ko ya ciyarda Miskinai guda shida, ko yayi Azumin kwana uku (3) a duk inda yaso. Saboda faden Manzan Allah Sallalahu Alaihi Wasallam ga Ka’ab dan Ujratu Allah yakara masa yarda: …………………………………………………