MARABA DA ZUWA SHAFINMU NA MUSULUNCI

29 Oct 2007

..... KE BATA ZUCIYA.....

Bismillahir Rahmanir Rahim
ABUBUWAN DA SUKE BATA ZUCIYA
Na: Imamu ibnul Qayyim
Imam ibnul Qayyim Allah yayi masa rahama yace: Amma abubuwan da suke bata zuciya guda biyar sune wanda yayi nuni akansu: yawan Cakud’a da mutane, da buri, da rataya da wani wanda ba Allah ba, da K’oshi, da barci. Wadannan sune manyan abubuwa guda biyar da suke bata zuciya.
NA FARKO: YAWAN CAKUDA DA MUTANE: Amma tasirin da yawan cakuda da jama’a yakeyi shine Zuciya zata cika da da Hyakin Numfashin Yan Adam har tayi bak’i, kuma hakan ze tilasta masa darewa da rabuwa da damuwa da bakin ciki,da rauni, da daukan abinda baze iya daukansa ba na takaicin Abokan banza, da bata abubuwan da zasu kawo masa amfani, da rafkana wato shagaltuwa daga barinsu, da wadansu al’amura, da kuma rarraba tunaninsa wajen nufinsu da nemansu, To menene yarage a wurinsa na ALLAH da ranar lahira?
* Wannan kenan, kuma dayawa daga cikin cakuda da mutane ya jawo bala’i, kuma yazama sanadin hana samun ni’ima, da saukar da Jarrabawa, da lalacewar dama, da musiba ta fad’o, kuma da aukuwan bala’i, kuma shin ba duk cutarwan dayake samun mutane ba, mutane ke zama sanadi?
* Kuma wannan cakuda da jama’an yana kasancewa ne wani nau’i ne na soyayya anan duniya, amma ze juye yazama Hukunci da gudun sashinsu daga sashi, idan kiyayya ta gaskiya ta tabbata, kuma me cakuda da jama’a ze cizi yatsa saboda nadama, kamar yanda Allah madaukakn Sarki yace: (“kuma a ranar da me zalunci yakeyin cizo akan hannayensa, yana me cewa: kaicona Inama da ace nabi tafarkin manzo! Ya kaicona! Inama! da ace ban riki wani masoyi ba! Tabbas, Hakika ya batar dani bayan tunatarwa tazo mini, kuma lallai Shed’an ya kasance ga mutum me zumbulewa.” Sur.Furqan 27-29) kuma madaukakin sarki yace: (Masoyan juna a wannan yinin, sashinsu mak’iyi ne ga sashe in banda masu tak’awa” (wato masu jin tsaoron Allah su masu san junane) Sur. zukhruf 67) kuma Badansa –wato Annabi Ibrahim- Yace: (“Babu abinda kukayi sedai kun riki gumaka saboda soyaiyar tsakaninku a cikin rayuwar duniya. Sa’an nan a ranar k’iyama sashinku ze kafirce ma sashi,kuma sashinku ze tsinewa (la’anta) sashi kuma makomarkun itace wuta, kuma Azzalumai basuda wadansu ma temaka” Sur. Ankabut 25)
* Kuma ma’auni me amfani a cikin cakudanya da jama’a: shine: yayi cakuda da mutane a cikin alkhairi, kamar Sallar juma’a da sallar Jam’i, da Iduka da Hajji, da koyan karatu da Jihadi, da yin Nasiha.
kuma ya kauracemasu a cikin aikata sharri, da halal din da baya da amfani.
* Idan bukata tasa shi haduwa da jama’a, ta yanda be sami daman kadaituwa daga garesu ba, to yaji tsoro kada ya goyi bayansu, kuma yayi hakuri akan cutarwan su, domin dole su cutar dashi, matukar beda karfi ko matemaki.
Sedai cutarwa ne da daukaka zata biyo bayansa, da soyayya agareshi, da girmamawa da yin yabo agareshi, daga wajen muminai da ubangijin halittu, kuma goyon bayansu kaskancine zebiyo bayansa da kiyyaiya gareshi, da Fushi da zargi daga wajensu, da muminai, daga ubangijin halittu. Saboda haka yin hakuri akan cutarwansu shine yafi alkhairi kuma yafi makoma me kyau, kuma yafi godiyan makoma.
* Kuma idan bukata tasa ya cakudu dasu a ckin halal da bashi da amfani, se yayi kokari ya juya wannan zaman yakoma yin biyyaiya ga ALLAH idan yasami dama.
NA BIYU: HAWA KAN TEKUN BURACE-BURACE:
Kuma shi kogine da beda tudu. Shi rafine wanda marasa rabo ke hawa daga cikin halittu, kaman yanda aka ce: guguwan burace – buracen karya, da tunanin banza, bazata gusheba, tana wasa da wanda ya hauta, kamar yadda karnuka ke wasa da gawan mamaci, kuma kaya ce na kowace rai, wulakantacciya kaskantacciya dake kasa, batada himman da za’a sami gaskiya da ita a fili, kai tasaba da burace –buracen kwakwalwa. Kuma kowanne da irin halinsa: daga me burin abin koyi da sarauta, da kuma Fatauci abayan kasa da zagaye – zagayen garuruwa, ko saboda dukiya da kudi, ko dan mata da yan samari, wanda yakeda burace – burace yana kama da wata sura da yake nema a cikin zuciyarsa wanda yasami rabo da samunsa, kuma yaji dadin samu rabo dashi, to yayin da yake a ckin wannan yanayi, se kawai yafarka se gashi akan tabarma!!
*To me himma datake babba, burace – buracensa sunna kewayawa ne a tsakanin da Ilimi da Imani, da yin aikin daze kusantashi zuwa ga Allah (Ubangijinsa) kuma ya matsar dashi zuwaga yin makwabtaka dashi. To burace – buracen wannan shine Imani da haske da hikma, amma burace –buracen wadancan zambace da rudu.
Kuma hakika manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yayi yabo akan masu yin buri na alkhairi, har ma yasanya ladan wanda yayin burin aikata aikin alkhairi kamar na wanda ya aikata din.
NA UKU: RATAYUWA DA WANDA BA ALLAH BA MADAUKAKIN SARKI: Kuma Wannan shine mafi girman abinda ke bata zuciaya kai tsaye, bashi da abinda yafi wannan cutarwa, kuma abinda yafi wannan yanke masa abubuwa masu amfani da tsira kamansa,domin idan har yaratayu da wanda ba Allah ba, Allah se ya dogarar dashi zuwa ga wannan abinda daya ratayu dashi, mutuwansa yasami abinda yakeso a wajen wanda ba Allah ba daya Ratayu dashi, da juyawarsa zuwa ga waninsa, shi din be sami rabonsa da yake wajen Allah ba, kuma be kai wajen abinda yake buri ba, da ya ratayu dashi. Allah madaukakin Sarki yace: (“kuma sun riki wadanda ba Allah ba (wato gumaka) a matsayin abin bauta don suzama matemaka a garesu, A’aha zasu kafircema ibadarsu, kuma su kasance mak’iya akansu” Sur. maryam 81 -82) kuma yace: (kuma sun riki wadansu abubuwan bautawa da ba Allah ba, sunyi tsammanin zasu temakesu. ( Bazasu taba iya temakonsu ba, alhali su din runduna ce daza’ akawosu (cikin wuta) Sur. Yasin 74 -75).
* Wanda yafi kowa kaskanci: shine wanda ya ratayu da wanda ba Allah ba, domi duk abinda yawuceshi na maslahohinsa da tsiransa da samun rabonsa, shine mafi girman abinda yasamu daga wanda ya rtayu dashi, shi yana fuskantar gushewa da kufcewa.
Kuma misalin wanda ya ratayu da wanda ba Allah kamar kwatankwacin wanda yake neman Inuwane daga zafi ko neman sanyi agidan gizo – gizo, mafi raunin gidaje.
* A dunkule: tushen shirka da K’a’idar da aka ginashi akanta: shine ratayuwa da waninda ba Allah ba. Kuma me yin hakan abin zargine kuma abin kaskanci, Allah madaukakin sarki yace: (“kada ka hada wani da Allah a wajen bauta, har kazauna kana abin zargi wulak’antacce” Sur. Isra’i -22) ma'anan abin zargi: bakada me gode maka, wulakantacce: kuma babu me temako agareka.
NA HUDU: ABINCI: Kuma abinci yana bata zuciya ta nau’i biyu:
Na d’aya: abinda ke bata zuciyan dakansa sune kaman abubuwan da’aka haramta. Kuma suma sun kasu kashi biyu: * Abubuwan da’aka haramta saboda Allah, kamar mushe, da Jini, danaman kare, da masuyatsu daga cikin dabbobi, da tsuntsaye masu k’unba. * Abubuwan da’aka haramta saboda bayi: kamar abinda aka sata,da wanda akayi kwacensa, da wanda akayi fashinsa, da duk wani abinda aka amsa a hannun meshi ba tareda izininsa ba, kodai fin karfi kokuma jin kunya da zargi.
Na biyu: Abinda ke bata wani sashi na zuciya kuma yawuce iyaka, kamar yin almubazaranci da abinda yake halal ne, da koshi wanda yawuce iyaka, domin ze hanashi yin abubuwan d’a a (biyaiya), kuma ya shagaltar dashi da cin abincin daze cika mai ciki sosai, yin kokari har se yasami hakan, kuma idan yasameshi, to ze hanashi (gudanarda hakan?) wato zesashi tumbi-da yin kariya daga abinda ze cutardashi, da cutuwa da nauyinsa, kuma abubuwan da sukesa sha’awa zasu yi k’arfi agareshi, kuma zebi hanyar shedan ya fadadata, domin yana gudu a jikin dan Adam kamar yadda jini ke gudu (yana bin hanyar jini ajikin dan adam). To Azumi kuma yana kuntatasu kuma ya yoshe hanyoyinsa, kuma duk wanda yaci abinci da yawa to ze sha ruwa da yawa, kuma zeyi barci me yawa kuma yayi asara me yawa. Kuma yazo cikin hadisi mashhuri: (“Dan Adam be cika mazubinsa- tumbinsa ba- da sharri fiyeda cikinsa, wasu y'an lomomi sun isa dan Adam wanda ze tsayu da doronsa ko bayansa. Idan kuma yakasance babu makawa, to daya bisa uku na abincinsa, daya bisa uku na abin shansa,daya bisa uku na numfashinsa,” Tirmidhi da Ahmad da Hakim)
NA BIYAR: YAWAN BARCI: Domin kashe zuciya,kuma yasa jiki yayi nauyi, kuma ya bata lokaci,kua nya gadar da yawan mantuwa, da kasala.
Kuma daga cikin barcin akwai wanda yake makaruhi ne (abinda aka kyamaci aikatashi) daga ciki akwai wanda yake cutarwa, wanda beda amfani da yake cutarda jiki, kuma barci mafi amfani: shine wanda akayishi lokacin tsananin bukatuwa zuwa gareshi. Da barcin Farkon dare, shine yafi amfani akan na karshensa,kuma barcin tsakiyar rana shi yafi amfani akan na farkonsa da na karshensa, kuma duk lokacin da barci yayi kusa da farkonsa ko karshensa, amfaninsa yana raguwa, kuma cutarwarsa yana karuwa, musamman ma dai barci da la’asar. Da barcin farkon rana sedai ga wanda beyi barci ba da daddare da yawa.
* Daga cikin makaruhinsa (barci) akwai: Yin barci tsakaicin sallar Asubahi da fitowar rana, domin lokacine da’ake samun Ganima (rabon arziki) kuma tafiya a wannan lokaci tanada fifiko me girma koda sun kasance sun kwana suna tafiya, ba'aso su tsaya a wannan lokacin har se rana ta fito, shine farkon Yini da mabudinsa, kuma lokacin saukowar arziki, da samun kaso, da saukar albarka. Kuma a cikinsa Yini ke farawa, kuma a lokacin ne ake janye hukuncin samun kason wannan yini. Saboda haka yakamata yin barci a cikinsa yazama ga wanda yazama masa dolene kawai wato kamar barcin wanda ya matsu.
* A dunkule matsakaicin barci da me anfaninsa shine,barcin a rabin lokacin dare na farko,da kuma karshensa, kuma shine kwatankwacin awa takwas. Kuma wannan shine mafi dacewar barci, kuma gwargwadan abinda ya karu akansa ko ya ragu, gwargwardan yadda zeyi tasiri a adabi’ance.
* Daga cikinsa akwai wanda beda amfani: shine yin barci a farkon dare, daf da faduwan rana har zuwa sanda duhun, Isha ze bace. Kuma Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yakasance yana kyamatarsa. To shi abin k’ine a shari’ance da kuma dabi’a. Allah ya temakemu.