29 Oct 2007
..... KE BATA ZUCIYA.....
at 11:24
6 Oct 2007
HUKUINCE HUKUNCEN SALLOLIN IDI (Karamar Sallah da Babba)ٍ
Dasunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai
SALLOLIN IDI GUDA BIYU
Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya shar'anta ma bayinsa yin Iduka guga biyu, sallar Idi guda biyu, Sune Sallar Idi Karama da Idi Babba
HUKUNCIN YINSU
Halartar Sallar Idi dai Sunnah ce, wacce take mekarfi wato kamar wajibi take, saboda Allah madaukakin Sarki Yayi Umarni dasu inda Yace: (Lallai ne mu munyi maka kyauta mai yawa, saboda haka kayi Sallah domin Ubangijinka, kuma kayi suka –wato sukan rakumi ko yanka- kenan.) Sur, kauthar.1-2
Kuma ya rataya samun rabo da ita inda yace: (Hak'ik'a wanda ya tsarkaka (da imani) yasami babban rabo, kuma ya ambaci sunan ubangijinsa sannan yayi sallah.)
LOKUTAN YINSU
Shine lokacin da rana ta fito sama gwargwadon dagawan mashi daga k'asa har zuwa lokacin Gushewar rana (zawali) amma abinda akafiso shine ayi Idi babba a farkon lokaci, saboda mutane su samu daman yanka layyansu, Idi karama kuma anfiso a jinkirta ta saboda mutane su sami daman fitar da zakkan kono. Yatabbata manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Yana yin hakan a Hadisin Jundub Allah yakara yarda agareshi.
LADUBBANSU DA ABUBUWAN DA SUKE MUSTAHABBAI ACIKINSU
1. Yin Wanka da Sanya turare da Sanya mafi kyawun tufafi. Saboda fadin Anasa Allah Yakara Yarda Agareshi Yace: (Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Ya Umarci mu da mu sanya mafi sabunta abinda muka samu , kuma mu sanya mafi kyawun turare, kuma muyi layya da mafi tsada daga abinda muka samu-wato muke dashi) Imamul Hakim.
Tunatarwa: Amma ba'a sanya jajayen kaya biyu wato taguwa da wanda, ko me ruwan rawaya guda biyu, saboda manzan Allah ya hana sa wadannan launukan, amma babu laifi idan guda dayane
2.Cin Abinci kafin fita zuwa Sallar Idi K'arama, Ranar Idi Babba kuma se idan andawo daga Idi sannan se aci daga abin Layya, wato yanka da mutum yayi. Saboda Hadisin Buraidah Allahn Yakara masa Yarda Yace: (manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Yakasance Baya yin Sammako a Ranar Idi K'arama har se yaci, -wato se yaci wani abu- kuma bayaci a Ranar Idi Babba har se yadawo, se yaci daga abin Layyansa.) Imamut-Tirmidhi
3. Yin Kabbarori tun daga daren Idi Karama da Idi Babba, na Idi Karama za'a cigaba dayi lokacin fitowa daga gida zuwa filin Idi, baza'a yanke ba har se Liman Ya'iso, snnan a yanke. A idi Babba kuma za'a cigaba dayi har zuwa kwanaki uku na Shanyan Nama wato na Layya, Ga Lafazin Kabbarorin: Allahu Akbar Allahu Akbar La'ilaaha illallaah, Allahu Akbar Allahu Akbar, Walillaahil Hamd. Kuma an karfafa san yinsu a lokacin fitowa daga gida zuwa Filin Idi, da Bayan Sallolin Farilla guda biyar, a kwanakin Idi babba saboda fadinAllah Madaukakin Sarki: (kuma ku ambaci Allah a cikin wasu kwanaki k'ididdigaggu) Sur. Baqarah-203.
Da fadansa ( kuma ya ambaci sunan Ubangijinsa Kuma yayi Sallah)
4. Fita zuwa filin Sallar Idi ta wata Hanya da dawowa ta hanya ta dabam wato sauya hanya kenan Saboda manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Yakasance yana aikata hakan kamar yadda Jabir yafada acikin hadisi Allah Yakara masa yarda. Bukhari ya ruwaitoshi.
5. Yin Sallar Idi a fili, se dai idan an samu ruwan sama, ko makamancinsa to se ayi a cikin masallaci. hakan Yazo cikin Hadisi ingantacce.
6. Yima juna Barka ko Murna da Idi, da fadin: TAQABBALAL LAHU MINNA WA MINKUM saboda Sahabban Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam sun kasance in sun sauko Idi suna fadama junansu Haka idan suka hadu ( taqabbalal lahu minna wa minkum) Imamul Baihak'i. Ma'ana Allah Ya Karba Mana Idinmu tare danaku.
7. Rashin Yin Almubazzaranci a abinci da abin Sha, das wasa wanda aka halasta, saboda fadin manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam: ( Ranakun Idi ranaku ne na ci da sha, da ambaton Allah Madaukakin Sarki ) Imamu Ahmad.
SHIN KO ANA YIN NAFILA KAFIN IDI KO BAYANTA?
Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yayi hani da yin Salla kafin Idi ko Bayanta kuma ba'ayin kiran Sallar Idi ko tada Ik'ama, haka kuma Sahabbansa.
SAURAREN KHUDUBA
Anaso ga Wanda ya halarci Sallar Idi da yatsaya ya saurari Khuduba domin akwai lada acikin hakan, amma anyi rangwame ga wanda beso yaji da yatafi batareda yatsaya yayi surutu ga masu sauraro ba, kuma haka anyi rangwame ga wanda yayi Sallar Idi base ya halarci juma'a ba, wato idan Idi ta kasance ranar juma'a kenan.
Ya Allah ka sanya ayyukanmu suzama saboda kai kuma ka karba manasu Amin.
at 18:33
4 Oct 2007
Yin Azumin Sittu Shawwal
Imamu Muslim ya fitar da Hadisi ingantacce Daga Abu Ayyub Al'ansari Allah Yakara Yarda agareshi daga ManzanAllah Sallallahu Alaihi Wasallam Yace: (Duk Wanda ya Azumci Ramadan Sannan Y bishi da Azumi Shida a cikin Shawwal ya kasance kamar wanda ya Azumci shekara) Muslim.
Azumin kwana shida na watan sallah wato watan shawwal kenan Mustahabbine, wannan shine zancen mafiya yawa daga cikin malamai, wasu kuma sukace makaruhi ne saboda jin tsoron kada a dauka cewa shima wajibi ne kamar na Ramadan.
Yadda Ake Azumtansa
Malamai sunyi zantuka guda uku (3) kamar haka:
1. Yin Azumin guda shida ajare a farkon watan.
2. Yin Azumin ajere ko a rarrabe duka daya ne a kowani lokaci a cikin wata.
Fa'idan Azumin Shawwal
1. Yin Azumi Shida na Shawwal yana Cika ladan Azumin shekara.
2. Azumin Shawwal kamar Sallolin Nafiloli ne da'ake yi kafin da bayan Sallaolin farilla. Wanda suke cika nak'asa da tasamesu
at 14:21
2 Oct 2007
I'ITIKAFI
I'ITIKAFI
Shine lazimtan masallaci da zama cikinsa da niyyan samun kusanci zuwa ga Allah. kuma malamai sunyi ittifak'I -wato sun hadu- akan cewa itikafi an shar'antashi kuma mustahabbi ne.
Tunatarwa: wasu mutane na kuskure ta yanda suke daukan cewa Itikafi, yakebanci manzan Allah ne Sallalahu Alaihi Wasallam shi kadai, wasu kuma suce hadisin Itikafi an shafe shi, wasu kuma suna dauka cewa Itikafi na dattawane ko akasin hakan, to duk wadannan kurakurai ne ba'a sha. Nana A'isha Allah yakara yarda agareta tace: (Lallai manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yakasance yanayin Itikafi a cikin goma na K'arshe na Ramadan har Allah yadauki ransa, sannan matansa sukayi Itikafi a bayansa) Bukhari. Ibn Hjar yace (Ba'a shafe hadisin ba kuma baya cikin abubuwan da suka kebanci ManzanAllah Sallallahu Alaihi Wasallam)fathul baari 4/272.
HUKUNCIN ITIKAFI
Mafi yawan malamai sun tafi akan cewa mustahabbi ne.
Imamu Malik Yace: (Nayi tunani akan al'amarin Itikafi, da abinda yazo akansa, da yanda musulmai suka barshi, tareda cewa manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, be kasance yabarshi ba, se naga cewa sun barshi ne saboda yanada wahala akansu.)
Imam Azzuhri Yace: (akwai mamaki a Al'amarin musulmi! Sun bar Itikafi, tareda cewa Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, be barshi ba tunda yazo Madinah , har Allah madaukakin Sarki yadauka ransa.)
SHARUDDAN ITIKAFI
1. MUSULUNCI: baya inganta ga wanda ba musulmi ba.
2. HANKALI: mahaukaci baya itikafi, saboda koda ibada ta wajibi bata zama dole akansu ba, andaga alkalami akansu.
3. NIYYA: sharad'I ce ga dukkan ibadodi, kuma duk aikmin da babu niyya a cikinsa ba karbabbe bane.
4. MASALLACI: ga namiji dolene yayi a masallaci, amma mace kuma anyi sabani akanta, Malam SUHNUNU Yace: (nace ma ibnul K'asim: menene zancen Imamu Malik gameda Itikafin mace tayi amasallacin jama'a? se yace Na'am, yace: a zancen Malik tayi Itikafi a masallacin gidanta? Se yace: Hakan baya burgeni, ana itikafi ne a masallacin da'aka yishi dan Allah.) Mudawwana 1/295.
Sheikh Aminul Hajj yace: (amma yafi rinjayen dalili awurina shine mace tayi Itikafinta a gidanta, wato wurin da takebance shi tana sallah a cikinsa.
5. AZUMI: wasu daga cikin malamai sukace kada mutum yayi itikafi face yaname Azumi, an tambayi Ibnul K'asim: (shin anayin itikafi batare da azumi ba a cikin zancen Malik? Se yace: ba'ayi se da Azumi. Wasu kuma sukace anayi koda mutum beyi Azumi ba, Sukace wannan shine ra'ayi mafi rinjayen dalili, saboda Hadisi Umar ingantacce da Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya Umarce shi da yayi itikafi yayin da yace masa yayi alwashin yin hakan a jahiliyya, kuma be ce masa yayi Azumi ba.
6. IZINI: dolene se miji yayi wa matarsa izini ko abinda ya mallaka na bawa ko baiwa, miji mace yana gida ne ko yayi tafiya dole tanemi izininsa, kuma idan yayi mata izini, to be kamata ya hanata ba kuma.
RUKUNNAN ITIKAFI
1.
ABUBUWAN DASUKE BATA ITIKAFI
1. FITA DAGA MASALLACI: baya halasta fita daga masallaci, In banda fita saboda: dan Biyan bukata kamar fitsari ko bayan gari, wankan janaba da na jumu'ah, cin abinci ko abin sha idan be iya ci ko sha a wurin da yake itikafi, idan yaji tsoron wuta ko sata kom rushewan gini, in aka fitar da shi da karfi, idan mace tayi haila da sharadin ta dawo da tayi tsarki, idan mijin mace yarasu ko yasake ta zata fita a mafi rinjayen zancen malamai biyu wasu sukace zata cigaba har seta kammala, fita saboda yin Umara, fita da mantuwa, idan yayi hauka ko suma.
2. YIN JIMA'I: saboda Allah yace: (kuma kada ku sadu dasu, alhalin kuna masu Itikafi a cikin masallatai…) Sur.Baqarah-186. haka sun bantan mace da sha'awa.
3. YIN RIDDA:wato fita daga musulunci
4. YIN MANYAN LAIFUKA: kamar yin zina da sata acikin itikafi, wanda mutane suna sakaci da daukan abin wani ko da kadan kuwa se a kiyaye.
5. YIN HAUKA KO SUMA: yana bata itikafi se dai idan yasami lafiya ko ya farfad'o to se yacigaba.
6. HAILA: idan mace tayi haila itikafinta ya baci, amma idan tayi tsarki se ta cigaba, na bayan be baciba.
ABUBUWAN DA BA'
Ba'aso me itikafi ya shagaltu da abinda ba ambaton Allah ba, da kuma abinda ba dolene ba.
1. jayayya. 2. zagi damaganganun banza. 3. Yin giiba da Annamimanci. 4. Kallon abinda yake haramun. 5. Rashin yin magana gaba daya tun daga safe har dare da sunan bauta.
Tunatarwa: wasu daga cikin daliban ilimi se kaga suna zuwa itikafi da wasu littafai na karatunsu suna yin muraja'a, ba haramun bane amma kamata yayi tunda kwanakine yan kadan a cikin shekara, meze sa bazakayi hakuriba, sauran kwanakin shekara kayi acikinsu.
ABUBUWAN DASUKA HALASTA GAME ITIKAFI
1. Yin wanka da canza kaya, da sanya kayan da yakeso.
2. Cin Abinci da Shan Abin Sha a cikin masallaci.
3. Yin magan da yan uwa, amma ba'ason yawaita surutu da mutane.
4.Ya nemi Aure ko a daura masa Aure.
5. Yin Aski da yanke Farce.
6. Sanya turare.
ABUBUWAN DA SUKE MUSTAHABBI GA ME ITIKAFI
1. Mustahabbi ne ga me itikafi, yakafa tanti da ze kangeshi daga jama'a, inbe samu ba se ya lazimce wurin da babu jama'a ta yanda baze barshi ba seda larura.
2. kiyaye yin Sallah cikin jama'a, da nafiloli.
3. Yawan karatun alk'ur'ani, da rashin shagaltuwa da abinda ba ruwa.
4. Yawan ambaton Allah, zikiri, da tasbihi.
5. Yin azumi a cikin wantan da ba ramadan, ga wanda zeyi itikafi da rana.
6. Yawan yin kokari wajen d'a'a.
MAFI KARANCIN ITIKAFI DA MAFI YAWANSA
Itikafin neman lada baya da kad'an ko mafi yawa, se dai wanda yayi Itikafi a goman k'arshe na Azumin kada ya fita se idan anga watan Sallah wato Shawwal, malamai sun hadu akan cewa baya da mafi yawa, amma sunyi maganganu akan karancinsa, wasu sukace mafi karancinsa Sa'a, wasu sukace Yini daya da dare, wasu sukace kwana goma.
Imamul k'urtabi yace: ( mafi karancin itikafi a wajen Malik, da Abu Hanifa, dare da yini….)
YAUSHE AKE SHIGA ITIKAFI KUMA YAUSHE AKE FITA
A. Shiga wajen itikafi:akwai zancen malamai guda biyu:
1. Shiga bayan sallar Asubahin ranar Ashirin da d'aya na Ramadan, saboda hadisin Nana A'isha Allah yakara mata yarda tace: (Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam idan ze shiga itikafi yana yin sallar Asubahi, sannan se yashiga wurin itikafinsa) Bukhari. kuma wannan shine mafi rinjayen dalili. Kuma mazhabinAhmad da Laith da Ishak'.
2. Shiga kafin rana r daren Ashirin da d'aya ta fad'i, wannan shine mazhabin Malamai hud'u
B. Fita daga itikafi: Ana fita daga wurin itikafi bayan ganin watan sallah, wasu kuma sukace mustahabbine ya
SIRRIN DA YAKE CIKIN I'ITIKAFI
Bauta tana da sirruka da hikimomi masu yawa, saboda ayyuka gaba daya, makewayansu itace Zuciya, kamar yanda Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Yace (..Kusaurara! lallai acikin jiki akwai wata tsoka wanda idan ta gyaru, to dukkan sauran jiki ya gyaru, kuma idan ta bace, to dukkan Sauran jiki ya baci, ku saurara! Itace zuciya.) Bukhari da Muslim.
To in muka duba zamuga cewa mafi yawan abubuwan da suke bata zuciya, sune sha'awan cin abinci da abin sha da saduwa da Iyali da Zancen da ba na dole ba, da barcin da ba na dole ba, da abokai da basu da wata fa'ida da sauran abubuwa dasuke kawar da zuciya daga yin abinda yake biyayya ne ga Allah, se Allah ya Shar'anta wasu abubuwa na lada da zasukare zuciya daga rud'ani da shagaltuwa daga ambaton Allah, kamar Azumi wanda yake hana mutum cin abinci da abin Sha da Saduwa da Iyali da rana. To wannan hanuwan daga wadannan abubuwan jin dadi, shine yake karfafa alak'a tsakanin mutum da Ubangijinsa, da fuskantar dashi ga Lahira, kena Azumi garkuwa ce datake kare zuciya daga abubuwan sha'awa da suke kawar da mutum daga yin biyayya ga Allah, duk da hanine wanda yake matsakaici saboda an halasta wa mutum wadannan abubuwa a cikin dare.
To haka shima Itikafi yanada Sirri me girma, shine Kare mutum daga yawan cakud'a da jama'a, da yawan magana, saboda me Itikafi yana shagaltuwane da karatun Alk'ur'ani da Tsayuwa –wato yin sallah- da Zikiri da yawan yin Addu'a da makamantansu, haka kuma akwai kariya daga yawan barci, tunda yazo ibada ne ba barci ba, to wadannan abubuwa barinsu shike kara sa zuciya ta fuskanci Allah.
ABUBUWAN TUNATARWA
* Wasu daga cikin malamai sun tafi akan cewa ba'ayin Itikafi se a masallatai guda Uku kamar yadda yazo a cikin Hadisi, na hani akan yin Itikafi a masallatan da basuba, manzan Allah Sallalahu Alaihi Waasallam yace (Babu Itikafi face a masallatai guda uku) imamu Tahawi. -Wato masallacin Harami wato Ka'abah da masallacin Madinah da masallacin Aqsa wato Kudus-, Malamai suka fassara shi da cewa hani ne na yin alwashin yin Itikafi a wani masallaci da tafiya zuwa gareshi saboda hakan se a wadannan masallatan kadai ya halatta, ayi hakan saboda duk malaman mazhabobi Hud'u sun hadu akan cewa ya halatta ayi a kowani masallacin Juma'a.
* wasu sukan bar ayyukansu na wajibi saboda suyi Itikafi, to yin hakan kuskure ne saboda shi Itikafi sunna ce, saboda haka ba'a barin abinda yake wajibi saboda Sunnah.
Ya Allah Ka Karba mana dukkan Ayyukanmu a cikin Watan Ramadana kasa Muna cikin Bayinka Yantattu dag Wuta kuma kadatarmu da daren Lailatul K'adari. Amiin
at 11:56